Saleh Mamman: An Samu Matsala a Zaman Shari'ar Tsohon Ministan Buhari
- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ɗage zaman sauraron shari'ar tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman zuwa ranakun 8 da 9 ga watan Mayu 2025
- An ɗage shari'ar ne bayan hukumar EFCC ta buƙaci hakan saboda rashin samun mai fassara, wanda zai riƙa yi wa wanda ake tuhuma bayani
- Hukumar da yaki da marasa gaskiya (EFCC) ce ta gurfanar da tsohon ministan kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi karkatar da dukiyar ƙasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shari’ar tsohon Ministan Makamashi, Injiniya Saleh Mamman, da ke gudana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake gamuwa da cikas.
Saleh Mamman ya rike kujerar minista ne a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an samu tsaiko a ci gaba da zaman shari'ar da ake tuhumar Saleh Mamman da sama da faɗi da dukiyar ƙasa a ranar Juma’a 2 ga Mayu, 2025.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta ƙara nakasa El Rufai da Kwankwaso, jiga jigai sun bar PDP da NNPP
Wane tsaiko aka samu a shari'ar Saleh Mamman?
An ruwaito cewa zaman ci gaba da sauraron shari'ar bai yiwu ba jiya Juma'a sakamakon rashin halartar mai fassara.
Lokacin da aka kira shari’ar, lauyan da ke wakiltar Hukumar EFCC, A. O. Mohammed, ya shaidawa kotu cewa sun gamu da cikas ne saboda rashin mai fassara.
Ya ce mai fassara ne zai taimaka masu wajen isar da bayanai ga wanda ake zargi da kuma tabbatar da fahimta tsakanin bangarorin biyu.
A cewarsa, ya samu labarin cewa mai fassara na kotun yana kan wani aiki na daban, don haka ya roki kotu da ta ba su karin lokaci domin lalubo mai fassarar da ya dace da shari'ar.
Lauyan wanda ake kara, Emmanuel Hassan, bai yi wata jayayya da bukatar dage zaman ba, inda ya goyi bayan rokon da lauyan EFCC ya gabatar.

Source: UGC
Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC
A nata bangare, Mai Shari’a James Omotosho ta amince da bukatar, inda ta dage sauraron shari’ar zuwa ranakun 8 da 9 ga watan Mayu, 2025.
Hukumar EFCC ce ta shigar da karar Saleh Mamman kan tuhume-tuhumr 12 da suka hada da hada baki domin aikata laifin sama da faɗi kudade da karkatar da wasu makudan kudade lokacin da yake minista.
A halin yanzu, ana sa ran cewa shari’ar za ta ci gaba da gudana a makon da ke tafe, yayin da jama’a da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da bibiyar lamarin.
EFCC ba za ta ƙyale kowane marasa gaskiya ba
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta bayyana cewa babu wanda za ta ƙyale matukar yana da kashin kaji a jikinsa.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede shi ne ya faɗi hakan da yake martani kan raɗe-raɗin da ake cewa hukumar za ta wanke tsohon gwamnan Delta daga zargi saboda ya koma APC.
Olukoyede ya kare yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta, ya ce shari’o’in rashawa musamman waɗanda suka shafi manyan ƴan siyasa, suna da sarƙaƙiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
