Tinubu Ya Yi Magana kan Rashin Ganin Buhari wajen Taron da Ya Je Katsina

Tinubu Ya Yi Magana kan Rashin Ganin Buhari wajen Taron da Ya Je Katsina

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya ji dadin tarayya da mutanen Katsina, amma yana kewar shugaba Muhammadu Buhari
  • Gwamna Dikko Radda ya karbi Tinubu cikin martaba tare da gudanar da liyafa a daren Juma'a, yayin da shugaban ke ziyarar kwana biyu a jihar
  • Shugabannin gwamnati da ‘yan kasuwa da sarakunan gargajiya sun halarci taron da aka shirya don karrama shugaban Najeriyan a Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana ci gaba da ziyarce-ziyarcensa zuwa jihohi domin kaddamar da muhimman ayyuka da ganawa da shugabanni da jama’a.

A wannan karon, shugaban kasar ya kai ziyara ta kwana biyu zuwa jihar Katsina inda ya samu tarba daga gwamnan jihar da sauran manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya.

Kara karanta wannan

"Karyarku ta sha Karya," Tinubu ya ɗauki zafi kan masu yunkurin tarwatsa Najeriya

Tinubu
Tinubu ya yi kewar Buhari a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Tashar NTA ta wallafa a X cewa shugaban kasar ya bayyana abin da ke zuciyarsa dangane da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda bai samu halartar taron ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce ya yi kewar Buhari a Katsina

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya ji dadin kasancewa cikin mutanen jihar Katsina da kuma liyafar da aka masa, amma yana kewar Muhammadu Buhari.

Bola Tinubu ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin gwarzon mutum mai riko gaskiya da amana.

Shugaban kasar ya ce:

“Na ci abinci mai dadi, kuma na ji dadin zama da mutanen Katsina. Abin da ya rage mani shi ne rashin haduwa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
"A matsayinsa na mutum mai gaskiya, ya kasance mai kaunar jihar nan kuma ya sadaukar da kansa wajen ci gaban Najeriya,”

Tinubu ya jaddada cewa ya na girmama tsohon shugaban bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen gina kasa da kare martabar al’umma.

Kara karanta wannan

2027: Daliban Arewa daga jihohi 19 sun gana da Atiku Abubakar a Abuja

Yadda Radda ya karbi bakuncin Tinubu a Katsina

Ziyarar kwana biyu da Tinubu ya kai a jihar Katsina ta hada da kaddamar da muhimman ayyukan raya kasa da gwamnatin Dikko Radda ta aiwatar.

A daren ranar Juma'a, Gwamna Dikko Umar Radda ya karbi bakuncin shugaban kasa a wani taron liyafa na musamman da aka gudanar a babban dakin taro na gwamnatin jihar Katsina.

Liyafar ta kasance cike da annashuwa da nuna al’adun jihar, inda aka gabatar da wakoki da abubuwan al’adun gargajiya domin karrama Bola Tinubu.

Rarara
Rarara ya yi wa Tinubu waka a Katsina. Hoto: ibrahim Kaulaha Mohammed|Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Manyan bakin da suka dura jihar Katsina

Liyafar ta samu halartar manyan baki daga bangarorin gwamnati, ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya da ‘yan kasuwa.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya jagoranci tawagar gwamnoni daga jihohi daban-daban.

Sun hada da Mai Mala Buni na Yobe, Mohammed Inuwa Yahaya na Gombe, Umar Namadi na Jigawa, Uba Sani na Kaduna da Aliyu Sokoto na jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

An lissafo ayyukan da Tinubu zai bude a Katsina a ziyarar da zai kai jihar

Haka zalika, mambobin majalisar zartarwa ta jihar Katsina, ‘yan majalisar dokoki, shugabannin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci sun halarci liyafar.

Bayan Katsina, Tinubu zai ziyarci Ogun

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasan Najeriya zai kai wata ziyara ta musamman jihar Ogun.

A yayin ziyarar, Bola Tinubu zai kaddamar da wani katafaren kamfanin sarrafa auduga mafi girma a duniya.

Gwamnatin jihar Ogun ta tabbatar da cewa kimanin mutane 250,000 ne za su samu guraben aiki a masana'antar da za a kaddamar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng