Rivers: An 'Kunyata' Matar Shugaba Tinubu yayin Gagarumin Taro, Mata Sun Yi Bore
- Wasu mata sun fita daga wajen taron tallafa musu da ake yi karkashin Sanata Remi Tinubu a Port Harcourt da ke Rivers
- Matan sun fice ne bayan an ba matar Kantoma abin magana, suka ce matar Fubara ya kamata ta yi jawabi ba Theresa Ibas ba
- Duk da zanga-zangar da suka yi a waje, an ci gaba da taron a ciki, inda Theresa Ibas ta wakilci Sanata Oluremi Tinubu
- An raba kayan tallafi kamar injin markade, murhu mai gas, injin nika da janareto ga mata 500 daga kananan hukumomi 23
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Wani dan karamin rikici ya faru ranar Juma’a a wajen shirin tallafawa mata na 'Renewed Hope Initiative' a Port Harcourt da ke jihar Rivers.
Wasu mata sun fice daga wajen taron da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta shirya a jihar.

Source: UGC
Yadda mata suka yiwa matar Tinubu bore
Channels TV ta ce matan sun nuna damuwa kan yadda matar shugaban rikon kwarya za ta yi jawabi maimakon matar Siminalayi Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suka ce matar gwamna da aka dakatar ya kamata ta yi musu jawabi, ba wata daban ba.
Wannan shiri ne na Sanata Oluremi Tinubu da aka shirya don rabawa mata 500 kayan sana’a tare da ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan SDGs.
Sai dai an samu tangarda lokacin da aka gayyaci matar mai rikon gwamnatin jihar, Theresa Ibas, domin gabatar da jawabi a wajen taron.
Wasu mata sun fara rera waka suna cewa:
"Ku dawo da Fubara, ba mu san Ibas ba."
Yayin da suke ci gaba da zanga-zanga a waje, an ci gaba da taron a ciki, inda matar mai rikon gwamnatin jihar ta yi jawabi.

Source: Facebook
Remi Tinubu ta yi magana kan tallafawa mata
A cewar matar Tinubu, an kammala irin wannan shiri a yankin Arewa ta Tsakiya, kuma wannan shi ne karshe a Kudu ta Kudu.
Remi Tinubu ta ce wannan shiri wani bangare ne na babban tsari na kasa da ke tallafawa mata 18,500 a sassa shida na Najeriya.
Kayan da aka raba sun hada da firiji, murhu mai gas, injin nika da janareto ga wadanda suka ci gajiyar shirin, cewar Leadership.
Ta ce:
“Wadannan kayan za su taimaka wa mata su kafa sana’o’i domin su taimaka wajen habakar tattalin arzikin kasa.
“Wannan shiri na cikin tsarin 'Renewed Hope' na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke mayar da hankali kan ci gaba mai dorewa da daidaito."
Ɗalibai sun 'kunyata' matar Tinubu
Kun ji cewa matar shugaban Najeriyar ta kai ziyara zuwa jihar Delta domin gabatar da shirin tallafi na 'Renewed Hope Initiative (RHI)' da take jagoranta.
Wani ɓangare na taron ya haɗa da rabon kayan aiki ga matan gwamnoni na yankin Kudu maso Kudu, waɗanda ke kula da shirin RHI a jihohinsu.
Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda daliban makarantar a suka ƙi amincewa da Remi Tinubu a matsayin “uwarsu.”
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

