Ranar Ma'aikata: Sababbin Bukatun da Kungiyoyin Kwadago Suka Tura ga Tinubu

Ranar Ma'aikata: Sababbin Bukatun da Kungiyoyin Kwadago Suka Tura ga Tinubu

  • Kungiyoyin kwadago sun bukaci Bola Tinubu ya soke dakatar da Gwamnatin Rivers da kuma cire dokokin haraji da ke gaban majalisa
  • Sun ce gwamnati ta daina daukar matakan da ke kuntatawa ‘yancin jama’a kuma ta tabbatar da gaskiya da adalci cikin mulki da zabubbuka
  • Kungiyoyin sun bukaci a dakatar da kashe-kashe da jini a kasa, tana mai cewa kare rayuka da dukiya na da muhimmanci fiye da komai
  • Sun kuma bukaci karin albashi, rage kudin wayar salula, biyan hakkoki da fansho, da daidaita albashi da hauhawar farashin kayayyaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta soke wasu matakai da ya dauka a Najeriya.

Kungiyoyin kwadago sun bukaci Tinubu ya soke dakatar da gwamnatin Rivers da aka yi ba bisa doka ba da kuma janye kudirin haraji.

Kara karanta wannan

An dakatar da manyan alkalan Najeriya 3, za su rasa albashin wata 12

Kungiyoyin kwadago sun sake taso Tinubu a gaba
Ana bikin ranar ma'aikata, kungiyoyin kwadago sun tura sababbin bukatu ga Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nigeria Labour Congress, NLC.
Source: Facebook

Wannan na daga cikin bukatun Shugaban NLC, Joe Ajaero da Shugaban TUC, Festus Osifo, a bikin Ranar Ma’aikata a filin Eagle, Abuja, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatun shugabannin kwadago ga Tinubu

Hakan ya biyo bayan bikin ranar ma'aikata da ake yi a yau Alhamis 1 ga watan Mayun shekarar 2025 a fadin Najeriya.

Ana yi bikin ne a kowace ranar 1 ga watan Mayu domin ma'aikata inda kungiyoyin kwadago ke neman sauyi a tsarin aikin gwamnati.

Shugabannin kwadago sun bukaci gwamnati ta daina gabatar da matakan da ke rage ‘yancin jama’a tare da inganta hadin kai da ci gaban kasa.

Sun bukaci gwamnati ta tabbatar da gaskiya da adalci, gyara harkar zabe, da kawo karshen danniya da hana mutane fadin albarkacin baki.

Kungiyar kwadago sun bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasa tare da kare rayuka da dukiyoyi.

Kungiyoyin kwadago sun yi magana kan kudirin haraji
Kungiyar kwadago ta bukaci Tinubu ya janye wasu matakai da ya ɗauka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Kungiyar kwadago ta shawarci Tinubu kan haraji

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi bayan kisan fitinannen ɗan bindiga da ya addabi Arewa

Game da kudirin dokokin haraji da ke gaban majalisa, kwadago ta bukaci a janye su domin bai wa ma’aikata damar shigar da ra’ayoyinsu.

A cewarsu, dokokin harajin sun bar attajirai da kamfanoni da kuma zama nauyi mai tsanani a kan ma’aikatan Najeriya.

A kan karin kudin wayar salula, sun bukaci a rage shi daga kashi 50 cikin dari zuwa kashi 35 cikin dari da gaggawa.

Bugu da kari, kungiyoyin kwadago sun bukaci a daidaita albashi da halin tattalin arzikin kasar da ma’aikata ke fuskanta yanzu.

Sauran bukatun sun hada da biyan dukkan hakkokin da aka ci bashi, dawo da fansho, karin shekarun ritaya da daidaita fansho da hauhawan kaya.

Tattaunawar Legit Hausa da ma'aikaci a Gombe

Abdulkadir Umar ya nuna takaici kan halin da ma'aikata ke ciki musamman tsadar rayuwa.

"Ya kamata gwamnatoci su duba yanayin halin da ake ciki musamman a Gombe duba da yadda muke dangwala yatsa kafin ka samu albashi."

- Cewar Umar

Malam Umar ya bukaci inganta rayuwarsu duba da muhimmancin ranar ma'aikata da aka gudanar.

Rivers: Kungiyar NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki

Kara karanta wannan

Portable: Bayan zayyano laifuffukansa, kotu ta tura fitaccen mawaki gidan kaso

Kun ji cewa Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani saboda dokar ta-baci da shugaban kasa ya ayyana a jihar Rivers.

Kungiyoyin sun bayyana cewa ayyana dokar ta jawo cikas ga biyan albashi, wanda ya jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali da korar masu zuba hannun jari.

Shugabannin kwadago sun bukaci Shugaba Bola Tinubu ya janye dokar ta-bacin, ko su dauki matakin da zai iya shafar tattalin arzikin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.