EFCC na Binciken CBEX kan Zambar N1.2trn, Manhajar Kirifto Ta Dawo Aiki a 'Ɓoye'

EFCC na Binciken CBEX kan Zambar N1.2trn, Manhajar Kirifto Ta Dawo Aiki a 'Ɓoye'

  • Manhajar CBEX ta dawo aiki a boye duk da binciken hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ke yi mata
  • Ana zargin CBEX, wani dandali na hada-hadar kirifto da tserewa kudin yan Najeriya wanda ya haura N1trn
  • Majiyoyi sun ce an goge tsofaffin asusun manhajar; an kunna sabon zaɓin cire kudi ga wadanda suka sayi jari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Manhajar hada-hadar kirifto ta CBEX da ke fuskantar zargi daga hukumar EFCC ta sake dawo da aikinta duk da binciken da hukumomin Najeriya ke yi a kanta.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) tana zargin manhajar da damfarar abokan hulɗarta, har ma an kaddamar da bincike.

Kirifto
CBEX ta dawo aiki a Najeriya Hoto; @abdullahayofel/@echoblognaija
Source: Twitter

Punch News ta ruwaito wasu ‘yan kasuwa guda biyu da ke amfani da dandalin CBEX sun tabbatar a ranar Laraba cewa manhajar ta sake bude kafarta a boye.

Kara karanta wannan

Portable: Bayan zayyano laifuffukansa, kotu ta tura fitaccen mawaki gidan kaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dawo hada-hadar CBEX

The Cable ta wallafa cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu haka manhajar CBEX ta dawo ba wa sababbin masu amfani damar yin rajista, kasuwanci da kuma cire ribarsu.

Bincike
Shugaban EFCC, Ola Olukayode
Source: Facebook

Daya daga cikin majiyoyin ta ce:

“Mutane yanzu na iya cire kudinsu daga CBEX. An dawo da zaɓin cire kudi. Amma bari in fayyace wani abu, an goge asusun tsohuwar manhajar gaba ɗaya; yanzu ba za ka iya cire kudi daga can ba."

EFCC na binciken manhajar CBEX

Majiyoyin sun bayyana cewa a halin yanzu ana gudanar da tantancewa ta inshora da kuma binciken lissafin kudi na kamfanin.

An gano cewa wata cibiyar kasashen waje ce ke yin aikin domin gano ainihin kuɗin da suka salwanta a shirin da ya durkushe a watan Afrilu. Sun kara da cewa masu zuba jari da dama da ba su samu damar karɓar kudinsu ba tsawon makonni, za su fara cire kudinsu daga ranar 25 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

A karshe, ISWAP ta dauki alhakin dasa bam da ya kashe mutane 26 a Borno

Wannan na zuwa ne kasa da wata guda bayan Hukumar lula da harkokin hannayen jari ta ƙasa (SEC) ta bayyana CBEX a matsayin haramtacce dandali.

Haka kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) , ta tabbatar da haramcin dandalin, kuma ta fara bincike a kai.

Su wanene CBEX?

CBEX, wani dandali ne na zuba jari a intanet da ke alkawarin riba mai yawa ga masu saka jari, inda ta ce tana bayar da riba 100% cikin kwanaki 30.

Manhajar ta fara aiki a shekarar 2024 bayan samun rajista daga hukumar rajistar kamfanoni (CAC) a ranar 25 ga Satumba, 2024.

Haka kuma ta samu sahalewar Ofishin Musamman na EFCC da ke yaki da safarar kudi ba bisa ka’ida ba (SCUML) a ranar 16 ga Janairu, 2025. Rahotanni sun nuna cewa sama da ‘yan Najeriya 600,000 ne suka saka jari a shirin kafin ya durkushe a ranar 14 ga Afrilu, 2025, inda suka yi asarar Naira tiriliyan 1.2.

EFCC ta fara neman jami'an CBEX

Hukumar EFCC ta ayyana wasu mutane takwas da ta ke nema ruwa a jallo bisa zarginsu da tallata wannan shiri da ake ganin tamkar tsarin zamba ne. Sun hada da Johnson Oteno, Israel Mbaluka, Joseph Michiro, Serah Michiro, Adefowora Olanipekun, Adefowora Oluwanisola, Emmanuel Uko da Seyi Oloyede. A ranar Litinin, Adefowora Abiodun, daya daga cikin manyan shugabanni da ‘yan kasuwa a dandalin, ya mika kansa ga EFCC domin amsa tambayoyi.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 9': Kotu ta yanke wa matashi hukuncin ɗaurin shekaru 63

Najeriya za ta ci kuɗin kirifto

A baya, kun ji cewa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake gurfanar da kamfanin hada-hadar kuɗin intanet na Binance Holdings Limited a gaban babbar kotun tarayya.

Gwamnatin tana neman a biya ta diyya har Dala biliyan 81 bisa zarge-zargen da suka haɗa da jawo wa ƙasar asarar tattalin arziki da kuma ƙin biyan haraji mai yawa.

FIRS da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) na zargin manyan jami’an kamfanin guda biyu, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da laifin safarar kudi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng