Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Yi Bankwana da Duniya

Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Yi Bankwana da Duniya

  • An shiga jimami a jihar Delta bayan an yi rashin babban dattijo kuma tsohon soja wanda ya hidimtawa Najeriya cike da sadaukarwa
  • Tsohon gwamnan soja na jihohin Cross Rivers da Akwa Ibom, Janar Paul Ufuoma Omu, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 84
  • A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa marigayin wanda ya riƙe muƙamai da dama ya rasu ya bar matarsa, ƴaƴa da jikoki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Tsohon gwamnan soja na jihohin Cross River da Akwa Ibom (wanda a baya ake kira jihohin Kudancin Gabas), Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu, ya rasu.

Iyalan marigayin ne suka bayyana rasuwarsa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom ya rasu
Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu ya rasu Hoto: Immanuel Penda
Source: Facebook

Sanarwar wacce Oghenekome Ufuoma Omu ya sanyawa hannu a madadin iyalan, ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne a ranar Talata, 29 ga watan Afrilu, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

Manjo Janar Paul Ufuoma Omu ya rasu

Marigayin yana da shekara 84 a duniya, kuma ya fito ne daga ƙauyen Igbide da ke ƙaramar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kafin rasuwarsa, ya yi aiki a muƙamai da dama a matakin ƙasa da kuma na yankinsa.

"Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu mutum ne mai son iyali, ɗan ƙasa na gari, ɗan siyasa, soja kuma jagoran al’umma wanda rayuwarsa ta kasance cike da jajircewa wajen hidimtawa Najeriya da ƙabilarsa ta Isoko."
“A matsayinsa na jami’in soja mai ƙwarewa, Janar Omu ya yi tashe a rundunar sojan Najeriya, inda ya hidimtawa ƙasa cike da ƙima da jajircewa."
“Ya riƙe muƙamai da dama na shugabanci da na gudanarwa, ciki har da kasancewa gwamnan soja na jihar Kudancin Gabas (wanda yanzu ta kasu zuwa Cross River da Akwa Ibom) daga watan Yuli 1975 zuwa Yuli 1978."
"A lokacin mulkinsa, ya ƙaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da sauye-sauyen manufofi da suka share fage ga ci gaban yankin."

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi yadda guguwar Tinubu ke shirin gamawa da PDP a Najeriya

“A fagen siyasa, Janar Omu ya taka muhimmiyar rawa a komawar Najeriya zuwa mulkin dimokuradiyya."
“Bayan hidimarsa a fannin soja da siyasa, Janar Omu ya ci gaba da nuna ƙwazo da kishin ci gaban ƙasarsa, musamman ƙabilarsa ta Isoko."
"Manjo- Janar Omu ya bar matarsa, Sanata Stella Omu, ƴaƴa shida, ƴan uwa, jikoki da dama da kuma ƙasa baki ɗaya da ke alhinin rashin ɗaya daga cikin ƴaƴanta masu daraja."

- Oghenekome Ufuoma Omu

Paul Ufuoma Onu
Manjo Janar Paul Ufuoma Omu ya rasu Hoto: Immanuel Pende
Source: Facebook

Iyalan marigayin sun bayyana cewa za a sanar da tsare-tsaren jana’iza daga baya.

Najeriya na rasa shugabanninta

A 'yan shekarun nan, Najeriya na ci gaba da rasa wasu daga cikin manyan shugabanninta na baya, ciki har da tsofaffin gwamnoni da manyan jami'an soja da suka taka rawar gani a tarihin kasa.

Wannan wani al'amari ne da ke tayar da hankali da kuma cusa jimami a zukatan 'yan kasa, musamman ganin irin gudunmawar da wadannan dattawa suka bayar wajen gina Najeriya.

Daya daga cikin irin wadannan manyan mutane da Najeriya ta rasa kwanan nan shi ne Manjo-Janar Paul Ufuoma Omu, tsohon gwamnan soja na jihohin Cross River da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Atiku a 2023 ya fadawa Shettima, Ganduje dalilin komawar shi APC

Janar Omu ya rasu yana da shekara 84, bayan ya shafe rayuwarsa yana hidimtawa kasa da kishin ƙabilarsa ta Isoko. Ya yi mulki a lokacin da ake tsarin soja, kuma ya gabatar da muhimman ayyuka na ci gaban al'umma.

Rasuwar irin wadannan shugabanni na jaddada bukatar tuna da girmama tarihin su, da kuma karfafa matasa wajen koyon darasi daga jajircewarsu.

Najeriya na bukatar sabbin jagorori masu kishin kasa kamar su. Tare da addu’ar rahama ga rayukansu, ya zama dole mu ci gaba da tuna da gudunmawarsu ga ci gaban ƙasa da daurewar rayuwa mai kyau.

Tsohon gwamnan jihar Oyo ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Chief Omololu Ogunloyo ya yi bankwana da duniya.

Marigayin wanda kuma shi ne Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife, ya rasu ne da safiyar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.

Chief Omololu Ogunloyo wanda ya taɓa zama shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan ya rasu ne ƴan kwanaki kaɗan kafin cikarsa shekara 90 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng