Kotu Ta Yi Zama, Za a Yanke Hukunci kan Tuhumar Ganduje da Karkatar da Kuɗin Kano
- Babbar kotun Kano ta sake zama kan shari'ar da ake tuhumar shugaban APC na ƙasa, Abdullahu Ganduje da karkatar da kuɗin al'ummar Kano
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta shigar da ƙarar, tana tuhumar Ganduje, matarsa da wasu mutum shida da haɗa baki wajen talauta baitul mali
- Bayan sauraron kowane ɓangare, kotun ta shirya yin hukunci kan korafin masu kara cewa ba ta da hurumin sauraron wannan shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Babbar Kotun Kano a ranar Talata ta dage yanke hukunci a shari’ar da Gwamnatin jihar ta shigar da tsohon gwamna kuma Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnatin Kano karƙashin jagoranci Gwamna Abba ta kai ƙarar Ganduje da wasu mutum bakwai, bisa zargin cin hanci, karkatar da kudaden jama’a da kuma almundahana.

Asali: Twitter
Channels tv ta tattaro cewa waɗanda ake ƙara sun hada da Ganduje, matarsa Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar da Jibrilla Muhammad
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun ne kamfanonin Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd, da Lasage General Enterprises Ltd.
Ganduje: Abin da ya faru a zaman kotu
A zaman kotun da aka gudanar, lauyoyin wadanda ake tuhuma sun gabatar da ƙorafe-ƙorafe na farko, inda suka kalubalanci hurumin kotun da kuma ƙarin lokaci don kare kansu.
Lauyan da ke wakiltar Ganduje, matarsa da wani Umar, Offiong Offiong (SAN), ya bayyana cewa sun shigar da ƙorafin farko na neman korar ƙarar tun 18 ga Nuwamba, 2024, tare da hujjoji guda 28.
Lauyan gwamnatin Kano, Adeola Adedipe (SAN), ya ce ƙorafin ba shi da tushe balle makama.
Ya bayyana cewa sun miƙa nasu bayanan kan bukatar da masu kara suka shigar tun 22 ga Oktoba, 2024, tare da hujjoji da bayanai da ke goyon bayan ci gaba da sauraron shari'ar.

Kara karanta wannan
Tsohon ciyaman da kansila sun rasu da mutanen gari suka yi gaba da gaba da ƴan bindiga
"Muna rokon kotu ta yi fatali da ƙorafin da waɗanda ake ƙara suka gabatar," in ji lauyan gwamnatin Kano.
Lauyoyin wasu daga cikin wadanda ake tuhuma, Adekunle Taiye-Falola da Sunusi Musa (SAN) su ma sun gabatar da ƙorafe-ƙorafe makamantan haka.
Kotu za ta yi hukunci a shari'ar Ganduje
Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta amince da buƙatar ƙarin lokaci ga ɓangarorin da ke cikin shari'ar.
Haka nan kuma ta ɗage yanke hukunci kan hurumin kotu na sauraron wannan ƙara zuwa wani lokaci, wanda ta ce za a sanar da kowane ɓangare nan gaba.
Hukuncin da kotun za ta yanke zai tantance ko shari’ar za ta ci gaba ko kuma a dakatar da ita a wannan mataki.
Gwamna Abba ya ba hadimansa umarni
A wani labarin, kun ji cewa a ƙoƙarin tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da dukiyar Kano, Gwamna Abba Kabir ya umarci hadimansa su bayyana kadarorin da suka mallaka.

Kara karanta wannan
Sanatan APC ya bugi kirji, ya fadi sabuwar jiha da gwamnatin Tinubu za ta kirkiro
Gwamnan ya umarci dukkan waɗanda ya naɗa a mukamai su cike fom din bayyana dukiyoyi da kadarorin da suka mallaka kafin hawa mulki a hukumar ɗa'ar ma'aikata.
Bayan haka kuma mai girma gwamnan ya karrama wasu shugabannin hukumomi 13 bisa jajircewarsu wajen sauke nauyin da ke kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng