Kano: Kotu Ta Hukunta Matashin da Ya Yi Yunkurin Cakawa Mahaifinsa Makami

Kano: Kotu Ta Hukunta Matashin da Ya Yi Yunkurin Cakawa Mahaifinsa Makami

  • Wata kotu a Kano ta fusata bayan an tabbatar da cewa wani matashi ya yi yunkurin hallaka mahaifinsa, saboda kawai ya hana shi kudin batarwa
  • Kotu ta yanke wa matashin hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari saboda yunƙurin kai wa mahaifinsa hari da almakashi a Fagge
  • Matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya haɗa da ɗaukar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma barazanar kisa
  • Alƙali ya ƙara masa tarar N20,000 da bulala 40, tare da yi masa ƙarin ɗaurin wata shida idan ya kasa biyan tarar da aka yanke masa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wata kotu da ke zamanta a yankin Mai Alluna cikin karamar hukumar Fagge a jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.

Kara karanta wannan

"Kai ne ka jawo": Atiku ya fadi alakar Tinubu da kisan gillar mutane 54 a Filato

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan an kama matashin laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami da kunduma masa ashariya.

Jihar
An hukunta matashin da ya so cakawa mahaifinsa makami Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Alƙali Nasir Ahmad ne ya yanke wannan hukunci bayan kotu ta tabbatar da cewa matashin ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da matashin ne bisa tuhuma uku: ɗaukar makami ba bisa ƙa'ida ba, barazanar kisa da kuma ɗura wa wani ashariya.

Kano: Matashi ya yiwa mahaifinsa rashin kunya

Lamarin ya faru ne a unguwar Fagge, inda matashin ya fara yiwa mahaifinsa rashin kunya saboda ya hana shi kuɗin kashewa.

Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya fusata matuƙa, daga bisani ya ɗauki almakashi da nufin zai caka wa mutumin da ya raine shi tun yana karami.

Matashi ya amsa laifinsa a kotu a Kano

Bayan an karanta masa takardar tuhumar a kotu, matashin ya amsa cewa ya aikata laifin. Wannan ya ba wa kotu damar yanke hukunci kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Tinubu kan harin Filato, gwamna, sojoji da 'yan Sanda sun yi zama

Kiyawa
An kama matashin da ya zagi mahaifinsa a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

A hukuncin da Alƙali Nasir Ahmad ya yanke, kotu ta ɗaure matashin na tsawon shekara biyu a gidan yari domin ya girbi abin da ya shuka.

Haka kuma, an ci shi tararsa N20,000 tare da ƙarin hukuncin ɗaurin wata shida idan ya kasa biyan tarar.

Bugu da ƙari, kotun ta yanke masa bulala 40 a matsayin horo da darasi gare shi da sauran matasa masu halin nuna wa iyayensu yatsa.

Za a taimaki iyalan 'Yan Kano da aka kashe

A baya, kun samu labarin cewa gwamnatin Edo, ta bayyana cewa za ta biya diyya ga iyalan mafarauta 16 da wasu ’yan sa-kai suka kashe yayin wucewa ta yankin Uromi na jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa mafarautan na hanyarsu ne daga Fatakwal zuwa Kano domin bikin Sallah tare da iyalansu, lokacin da aka kai musu hari da kisa maras tausayi.

Ana zargin wata ƙungiyar sa-kai ta jihar ce ta aikata wannan danyen aiki da ya girgiza ƙasa baki ɗaya, inda ta mika wa mutanen gari mafarautan, kuma aka banka masu wuta har suka rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng