Ana Murnar Sauƙi Ya Fara Samuwa, Farashin Kayayyaki Ya Tashi a Najeriya

Ana Murnar Sauƙi Ya Fara Samuwa, Farashin Kayayyaki Ya Tashi a Najeriya

  • Kamar yadda ta saba a tsakiyar kowane wata, hukumar NBS ta fitar da alkaluman hauhawar farashin kayayyaki na watan Maris da ya gabata
  • NBS ta bayyana cewa farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 24.23% a watan Maris idan aka kwatanta da 23.18% da aka samu a Fabrairu
  • Wannan ne karo na farko da farashin kayayyaki ya karu tun da hukumar NBS ta fara amfani da ma'aunin farashi watau CPI a farkon 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 24.23% a watan Maris 2025.

Wannan alkaluma da hukumar NBS ta fitar ya nuna cewa an samu karin kashi 1.05.% idan aka kwatanta da kashi 23.18% na watan Farbarirun 2025.

Kara karanta wannan

DisCos sun lafto kudin shan wuta, Mataimakin gwamna ya koka da tsadar lantarki

Kayayyaki.
Farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 24.23% a watan Maris, 2025 Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta tataro cewa hakan na ƙunshe ne a rahoton da hukumar ta fitar ranar Talata, 15 ga watan Afrilun, 2025 kamat dai yadda ta saba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin kayayyaki ya tashi karon farko a 2025

Rahoton NBS ya nuna cewa wannan shine karo na farko da aka sake samun ƙari a farashin kayayyaki tun bayan da hukumar ta fara amfani da ma'aunin hauhawar farashi watau CPI a farkon 2025.

"A watan Maris 2025, hauhawar farashin kayayyaki ya karu da kashi 1.05% idan aka kwatanta da watan Fabrairu.
"A ƙididdigar wata-wata kuma, hawan ya kai kashi 3.90%, a watan Maris, wanda ya haura kashi 2.04% da aka samu a watan Fabrairu da kashi 1.85%.”

- Cewar rahoton kididdigar NBS

Hukumar NBS ta jero muhimman bangarorin da suka fi jawo hauhawar farashin wanda suka haɗa da abinci da lemukan kwalaba (9.28%), kuɗin hayar gida da wuraren cin abinci (2.99%).

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya kunyata masoya, ya hana fara yi masa Kamfen a dukkan jihohi

Sauran sun kunshi harkokin gidaje, wutar lantarki, gas da man fetur (1.95%), sufuri (2.47%), ilimi (1.44%) da lafiya (1.40%).

Kayan abinci.
Farashin kayan abinci ya ƙaru a Najeriya Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Farashin abinci ya ƙaru a watan Maris

Alƙaluman NBS sun kuma nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara ya tashi zuwa 21.79%.

Haka nan ta ce alkaluman wata wata na hauhawar farashin abinci ya ƙaru zuwa 2.18% a watan Maris, wanda ya fi kashi 1.67% da aka samu a watan Fabrairu.

Hukumar ta danganta ƙarin hauhawar farashin da tashin da aka samu a farashin wasu muhimman kayan abinci da suka hada da Sabuwar citta, garin rogo (ja), shinkafa, zuma, dankalin turawa, garin ayaba, ganda, da barkono.

Ɗangote ya rage farashin man fetur

A wani labarin na daban, kun ji cewa matatar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta rage farashin kowace litar man fetur daga N888 zuwa N865.

Hakan dai ya nuna cewa an samu saukin N15 idan aka kwatanta da yadda matatar Ɗangote ta sayar da kowace litar mai a ranar Larabar da ta gabata a kasar nan.

Wannan ragi da Ɗangote ya yi na zuwa ne sa'o'i ƙalilan bayan gwamnatin tarayya ta amince a ci gaba da tsarin sayar da ɗanyen mai da kuɗin gida Najeriya watau Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262