Tsohon Ciyaman da Kansila Sun Rasu da Mutanen Gari Suka Yi Gaba da Gaba da Ƴan Bindiga

Tsohon Ciyaman da Kansila Sun Rasu da Mutanen Gari Suka Yi Gaba da Gaba da Ƴan Bindiga

  • Mummunan harin da ƴan bindiga suka kai kauyen Morai da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara ya yi ajalin mutane biyar
  • Bayanan da ke kara fitowa daga majiyoyi masu karfi sun nuna tsohon kantoman Talata Mafara, Hon. Saminu Morai na cikin waɗanda aka kashe
  • An ruwaito cewa mutanen gari sun fito sun gwabza da maharan waɗanda ake zargin Fulanin yankin ne suka gayyato su kan taƙaddamar filaye

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Tsawon awanni uku wasu ƴan bindiga suka shafe suna aikata ta'addanci kan al'ummar garin Morai da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a Zamfara

Maharan sum yi wa garin kawanya, suka ci karensu babu babbaka tun daga karfe 1:00 na tsakar dare har zuwa karfe 3:15 na wayewar garin Litinin, 15 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Tinubu kan harin Filato, gwamna, sojoji da 'yan Sanda sun yi zama

Taswirar Zamfara.
Tsohon Kantoma da Kansila na cikin waɗanda aka kashe a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An kashe tsohon kantoma, kansila a Zamfara

A wani rahoto da Zagazola Malama ya wallafa a shafin X yau Talata, ya ce ƴan ta'addan sun kashe mutane biyar a harin, ciki har da tsohon kantoma da tsohon kansila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin kuma mai sharhi kan harkokin tsaro ya ce tsohon shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara na riƙo watau kantoma, Hon. Saminu Morai na cikin waɗanda aka kashe.

Ya ce harin wanda ya faru da misalin karfe 1:00 na dare, ya dauki sama da sa’o’i uku, inda aka yi arangama mai tsanani tsakanin ƴan bindiga da mazauna garin.

Bayan tsohon kantoma da aka kashe, an ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da tsohon kansila a karamar hukumar, Alhaji Akilu Liman.

Asalin abin da ya jawo rikici a Morai

Rahotanni sun ce maharan sun fito ne daga Bayan Ruwa, wani sansanin ‘yan bindiga a karamar hukumar Maradun, kuma ana zargin fulanin Jandutsi ne suka gayyato su.

Kara karanta wannan

Rogo ya jawo 'dan shekaru 49 ya sassara mahaifiyarsa da adda har barzahu

Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne daga zargin cewa shugaban karamar hukumar Talata-Mafara ya raba filayen kiwo da ke da alaka da gandun Jandutsi ga manoma Hausawa ba bisa ka’ida ba.

Haka nan an ce an sayar da kowane fili akan ₦50,000 ga manoman, abin da ya haifar da husuma tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma.

Fulanin Jandutsi sun zargi shugabannin yankin da cin hanci da rashawa da kuma ƙwace masu hakkinsu, suna mai cewa sayar da filin kiwon ya kassara rayuwarsu da kuma ta dabbobinsu.

Dauda Lawal.
Jami'an tsaro sun fara bincike kan harin da aka kai garin Morai Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Wannan lamarin ya haifar da wani rikici mai muni wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama.

Rahoton ya kara da cewa jami’an tsaron hadin gwiwa sun fara bincike a yankin domin kamo wadanda suka kai harin da kuma dawo da zaman lafiya.

An birne gawarwakin wadanda suka rasu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Yan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani rahoton kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai sababbin hare-hare a yankin ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara.

Ana zargin waɗannan hare-hare da ƴan ta'addan suka kai na da alaƙar da kokarin ɗaukar fansa kan kashe manyansu da jami'an tsaro suka yi a baya-bayan nan.

Ƴan bindigan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da sama da mutum 60, a hare-haren ta'addancin da suka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng