Kisan Mutane Sama da 50 Ya Girgiza Kwankwaso, Ya ba Gwamnatin Najeriya Mafita
- Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tir da kisan mutane sama da 50 a hare-haren ta'addancin da aka kai kwanan nan a Filato
- Tsohon gwamnan jihar Kano kuma mai neman shugaban kasa ya bukaci gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyi
- Kwankwaso ya kuma mika sakon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Filato tare da yin kira ga hukumomi su kamo tare da hukunta masu hannu a lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - 'Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan rikicin da ke faruwa a jihar Filato.
Kwankwaso ya bukaci hukumomi da su dauki mataki cikin gaggawa wajen cafke da hukunta wadanda ke da hannu a mummunan kisan gillar da aka yi a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Asali: Facebook
Jagoran NNPP ya bayyana hakan da yake nuna damuwa kan kashe-kashen da aka yi a Filato kwanan nan a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya sa baki kan rikicin Filato
Kwankwaso, wanda ya taba zama gwamnan jihar Kano har sau biyu, ya nuna bakin cikinsa kan harin da aka kai wa al'ummar Zike, Kimakpa a yankin Kwall, karamar hukumar Bassa.
Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 51 tare da kone-konen dukiyoyi da dama a jihar Filato.
“Na yi matukar bakin ciki da jin labarin harin da aka kai kauyen Zike, yankin Kwall a karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 51 da kuma lalata kadarori da dama.”
Tsohon gwamnan ya kara da cewa wannan hari ya biyo bayan wasu munanan hare-hare da suka yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane da dama cikin mako guda a wasu sassa na jihar.
Kwankwaso ya ce bai kamata a sake komawa zamanin tashin hankali da barna ba bayan an samu dan zaman lafiya a jihar Filato a 'yan shekarun baya.

Asali: Twitter
Wace mafita Kwankwaso ya ba gwamnati?
Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan ta’asa sun fuskanci hukunci.
“Ina mika ta’aziyyata ga gwamnati da mutanen Jihar Filato, tare da kira ga daukacin al’umma da su rungumi zaman lafiya.
"Haka nan ina kira ga hukumomi su tabbatar da an dauki mataki tare da hukunta duk masu hannu a wannan aika-aika,” in ji Kwankwaso.
Filato: Gwamna ya zauna da hukumomin tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya jagoranci zaman kwamitin tsaro kan kashe-kashen da ke faruwa a jihar.
Gwamna Mutfwang ya ce ‘yan bindiga sama da 100 ne suka afka wa wata ƙaramar al’umma a karamar hukumar Bassa da misalin ƙarfe 12:00 na dare.
Ya ce gwamnatinsa na ci gaba ɗaukar matakan gaggawa da tsauraran matakai na tsaro domkn daƙiƙe faruwar haka nan gaba, ya kuma roki jama’a su taimaka da bayanan sirri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng