Bayan Gargadin Tinubu kan Harin Filato, Gwamna, Sojoji da 'Yan Sanda Sun Yi Zama

Bayan Gargadin Tinubu kan Harin Filato, Gwamna, Sojoji da 'Yan Sanda Sun Yi Zama

  • Fiye da ‘yan bindiga 100 ne suka kai mummunan hari a wani ƙauye da ke karamar hukumar Bassa a Jihar Filato, suka kashe mutane da dama tare da kona gidaje
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya jagoranci taron kwamitin tsaro na musamman da ya haɗa da shugabannin tsaro da shugabannin kananan hukumomi don duba lamarin
  • Ya ce gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa da tsauraran matakai don hana maimaituwar haka, ya bukaci jama’a su rika bayar da bayanan sirri ga hukumomi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bassa a tsakar daren ranar Lahadi, 14 ga Afrilu, 2025.

An ruwaito cewa harin ya dauki hankali a fadin Najeriya kasancewar ya janyo asarar rayuka da barna mai yawa.

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: An ba malaman gona babura 300 domin shiga lungu da sako a Jigawa

Caleb
Gwamnatin Filato ta yi zama kan matsalar tsaro. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Twitter

Gwamnan ne da kansa ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a X bayan kammala wani taro na musamman da kwamitin tsaro da shugabannin kananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki tuƙuru domin gano musabbabin harin tare da ɗaukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan a gaba.

Bayani kan harin da aka kai Bassa

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa fiye da ‘yan bindiga 100 ne suka afka wa wata ƙaramar al’umma a karamar hukumar Bassa da misalin ƙarfe 12:00 na dare.

A cikin wani jawabin da ya yi, gwamnan ya ce:

"Sun yi mummunan ta’adi da asarar rayuka da dama da kuma kone-konen gidaje,"

Ya ce hukumomin tsaro sun bayar da cikakken bayani kan harin, kuma gwamnatin jihar ta fara ɗaukar matakan da suka dace don dakile barazanar hari a gaba.

Halin da aka shiga a Bassa bayan harin

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Gwamna Mutfwang ya ce yanzu haka an samu kwanciyar hankali a yankin da aka kai harin, kuma sun samu haɗin kan matasan yankin wajen kauce wa ramuwar gayya.

Caleb Mutfwang ya ce:

“Mun shawarci jama’a su kwantar da hankali, kuma muna godiya matuƙa da yadda matasa suka karɓi wannan kira da zuciya ɗaya,”

Ya kuma ƙara da cewa za a fitar da cikakken bayani kan matakan da gwamnati za ta ɗauka a cikin jawabin da zai gabatar a gaba.

Caleb
Gwamnan Filato ya ce hankali ya kwanta a Bassa bayan kashe kashe. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Facebook

An bukaci taimako wajen bayar da bayanai

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika bayar da muhimman bayanan sirri da za su taimaka wajen hana irin harin.

A ƙarshe, Gwamna Mutfwang ya roƙi Allah ya jikan waɗanda suka mutu tare da bai wa iyalansu haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure rashin.

Bukatar gyara a harkar tsaron Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilai mai lura da kwamitin sojin kasa a Najeriya ya bukaci a yi gyara a harkar tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

'Dan majalisar ya bayyana cewa akwai bukatar gyara na musamman a kan yadda 'yan banga ke aiki a fadin kasar nan.

Ya yi magana ne bayan an zargi wasu 'yan banga da hannu a kashe 'yan farauta da suka taso da Kudu zuwa Arewacin Najeriya a jihar Edo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng