Bayan Kashe Mutane 54 a Jihar Filato, Tinubu Ya Fadawa Gwamna abin da Zai Yi

Bayan Kashe Mutane 54 a Jihar Filato, Tinubu Ya Fadawa Gwamna abin da Zai Yi

  • Shugaba Bola Tinubu ya nuna bakin cikinsa kan harin da aka kai jihar Filato wanda ya yi sanadin rasa rayukan fiye da mutane 40
  • Tinubu ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang da ya jajirce wajen warware rikicin Filato, yana mai bukatar a dawo da zaman lafiya a jihar
  • Kungiyar Amnesty ta ce mutane 54 aka kashe a sabon harin, inda ta bukaci gwamnati ta kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Filato

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa kan harin kisan gillar da aka kai a jihar Filato, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 40.

Shugaban ya yi Allah-wadai da wannan tashin hankali, tare da mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, gwamnatin jihar da daukacin al’ummar Filato.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

Tinubu ya yi magana kan harin da aka kai Filato da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang (Hagu), Shugaba Bola Tinubu (Dama). Hoto: @aonanuga1956, @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana kaduwar Tinubu kan wannan harin a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da harin Filato

A cikin sanarwar, Shugaba Tinubu ya bukaci Gwamna Mutfwang da ya jajirce wajen kawo karshen rikicin tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

A cikin sakonsa ga al’ummar jihar Filato, Tinubu ya jaddada muhimmancin kaunar juna da hadin kai ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Ya bukaci shugabannin al’umma, addini da siyasa a ciki da wajen jihar da su hada kai don kawo karshen hare-haren ramuwar gayya da suka addabi yankunan da abin ya shafa.

Sanarwar ta rahoto Shugaba Tinubu yana cewa:

“Ya zama dole a dakatar da wannan rikici da ke faruwa tsakanin al’ummomin jihar Filato wanda ya samo asali daga kabilanci da bambancin addinai.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

“Na umurci jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan tashin hankali."

Tinubu ya fadawa gwamnan Filato abin yi yi

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba, yana mai cewa, "Ya isa haka.”

Sanarwar ta ci gaba da ruwaito maganganun Tinubu, inda ya kara da cewa:

“Baya ga hukunta wadanda suka aikata kisan, akwai bukatar shugabannin siyasa a jihar, musamman Gwamna Caleb Mutfwang, su duba asalin tushen wannan matsala ta shekaru fiye da ashirin.
“Na tattauna da gwamnan a lokuta daban-daban game da rikicin, inda na ba shi shawarwari masu amfani don samun zaman lafiya mai dorewa.
“Gwamnatin tarayya na nan daram wajen tallafa wa Gwamna Mutfwang da gwamnatin jihar Filato wajen inganta tattaunawa, karfafa hadin kai da tabbatar da hukunta masu laifi."

Amnesty ta fitar da rahoto kan harin Filato

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

Game da adadin mutane da aka kashe a harin da aka kai Filato, kungiyar Amnesty International ta ce mutane 54 ne aka yi wa kisan gilla a sabon harin.

A rahoton da ta fitar a shafinta na X, Amnesty ta ce daruruwan mutane ne aka raba da muhallansu, yayin da ake zaman dari-dari kan yiwuwar afkuwar wani sabon harin.

Amnesty ta bayyana cewa, 'yan ta'adda sun kashe akalla mutane 1,336 yayin da aka raba mutane 29,554 da muhallansu a Filato daga Disambar 2023 zuwa Fabrairun 2024.

Kungiyar da ke kare hakkokin dan Adam ta kasa da kasa, ta nemi gwamnatocin Najeriya da su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.

Gwamna ya fadi masu daukar nauyin harin Filato

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya yi tsokaci da ƙarfi game da hare-haren da ke ci gaba da addabar wasu ƙananan hukumomi a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan zuwan tawagar Kano, Okpebholo ya fadi yadda tinubu ya ji kan kisan ƴan Arewa

Ya bayyana cewa hare-haren ana kai su ne da nufin kawar da dangi gaba ɗaya, inda ake hallaka mutanen da ba su da laifi.

Gwamnan ya zargi wasu da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda domin tayar da zaune tsaye a jihar, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel