Rogo Ya Jawo 'Dan Shekaru 49 Ya Sassara Mahaifiyarsa da Adda har Barzahu
- Rundunar ‘yan sanda ta kama wani Nnamdi Anyaji, mai shekaru 49, bisa zargin kashe mahaifiyarsa, Dorathy Anyaji mai shekaru 68
- Mummunan al'amarin ya afku ne a kauyen Amudo a Ekwulobia na karamar hukumar Aguata da ke jihar Anambra saboda kudin kasuwancin rogo
- Maƙwabta ne suka fara ganin abin da ya faru, tare da hana Nnamdi hallaka kansa, sannan suka mika shi ga ‘yan sanda bayan ya yi barnar
- Rundunar ta tabbatar da kwato adda da ake zargin ya yi amfani da wajen kashe mahaifiyarsa, za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra - Rundunar ‘yan Sandan jihar Anambra ta kama wani mutum mai suna Nnamdi Anyaji bisa zargin kashe mahaifiyarsa tare da yunkurin kashe kansa.
Anyaji, mai shekaru 49, ɗan asalin ƙaramar hukumar Aguata ta Anambra, ya kashe mahaifiyarsa Dorathy Anyaji, wacce ke da shekaru 68, sannan ya yi ƙoƙarin kashe kansa bayan haka.

Asali: Original
Jaridar Punch ta ruwaito cewa maƙwabta ne suka tarar da shi yana ƙoƙarin hallaka kansa, suka hana shi, sannan daga bisani suka miƙa shi ga ‘yan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin ya kashe mahaifiyarsa ne sakamakon gardama da ta ɓarke tsakaninsu kan rabon kuɗin da aka samu daga kasuwancin rogo.
'Yan sanda sun kama matashin a Anambra
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da kama wanda ake zargin.
Ikenga ya ce:
“Jami’an ‘yan sanda da ke ƙarƙashin ofishin Ekwulobia sun kama Nnamdi Anyaji, mai shekaru 49 daga kauyen Amudo a Ekwulobia, wanda ya yi ƙoƙarin kashe kansa bayan ya kashe mahaifiyarsa, Misis. Dorathy Anyaji mai shekaru 68 a adireshin ɗaya.”

Kara karanta wannan
Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata
'Yan sanda sun kwace makami
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa sun kwato wata adda daga wajen da lamarin ya faru, wanda ake zargin Nnamdi ya yi amfani da shi wajen kisan.

Asali: Facebook
Ikenga ya ce:
“Jami’an tsaro sun kwato adda daga wurin da lamarin ya faru. Binciken farko ya nuna cewa rigimar ta ɓarke ne bayan wanda ake zargi ya tuhumi mamaciyar da rashin gaskiya kan kuɗin da suka samu daga kasuwancin rogo.
“A halin yanzu, wanda ake zargin yana tsare tare da kulawa ta musamman don hana shi kashe kansa, kuma za a gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike.”
Matashi ya kashe mahaifiyarsa da sanda
A baya, mun wallafa cewa qani matashi mai suna Mathias Amunde ya shiga hannun rundunar ‘yan sanda a jihar Kuros Ribas bisa zargin kashe mahaifiyarsa ta hanyar make ta da sanda.
Bayan kisan, an ce Mathias tare da wani abokinsa mai suna Walcot sun jefa gawar mahaifiyar tasa a cikin rijiya domin ɓoye mummunan aikin da suka aikata, amma asirinsu ya tonu.
Bayan haka, an bayyana Mathias ya amsa zargin da ake masa, Walcot kuma ya tsere daga wurin da abin ya faru, yayin da jami'an tsaro suka fara bincike domin a hukunta su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng