Portable: Ƴan Sanda Sun Kama Fitaccen Mawakin Najeriya, An Ji Laifin da Ya Aikata

Portable: Ƴan Sanda Sun Kama Fitaccen Mawakin Najeriya, An Ji Laifin da Ya Aikata

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama mawaki Portable a Abeokuta, bisa umarnin kotu bayan karar da Saheed Osupa ya shigar a Ilorin
  • Kakakin ‘yan sanda ta ce laifin ya hada da bata suna, barazana, tayar da husuma da kuma cin mutunci, an dauki bayanansa a gaban lauyoyi
  • Portable ya taba neman afuwa ga Osupa a bidiyo, yana cewa rikicin tallata juna ne. Amma daga bisani ya janye nadamar bisa matsin Osupa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun kama fitaccen mawakin Najeriya, Habeeb Okikiola Badmus wanda aka fi sani da Portable.

An kama mawaki Portable ne ne bayan wata kara da fitaccen mawakin Fuji, Okunola Saheed wanda aka fi sani da Osupa ya shigar.

'Yan sanda sun yi magana da suka cafke mawaki Portable
'Yan sanda sun cafke mawaki Portable bayan wani mawaki ya shigar da shi kara. Hoto: @Kwara_PPRO
Asali: Twitter

Kwara: An yi karar mawaki Portable

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta fitar a shafinta na X, Osupa ya zargi mawaki Portable da aikata laifuffuka masu nauyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin laifukan sun hada da bata suna da gangan, barazana ga rayuwa, tayar da husuma, cin mutunci, da daukar matakan da ka iya haddasa rikici a cikin al’umma, da amfani da kalmomin batanci da cin zarafi.

Wannan lamari ya kara dagula rikicin dake tsakanin wadannan fitattun mawaka biyu.

Dakarun 'Yan sanda sun cafke Portable

Sanarwar SP Adetoun Ejire-Adeyemi ta ce:

“Dangane da nauyin wadannan zarge-zarge da kuma shaidu masu karfi da aka gabatar, rundunar ta samu sahalewar kotun Majistare mai zama a Ilorin domin kama wanda ake zargi.
“Da wannan umarni, jami’an rundunar suka nufi Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Lahadi, 13 ga Afrilu, 2025, inda aka kama wanda ake zargi da misalin karfe 7:25 na yamma.
“Nan take aka tafi da shi Ilorin domin ci gaba da bincike. Bayan ya isa, an dauki bayanansa a gaban lauyoyin bangarorin biyu.”

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

Ejire-Adeyemi ta ce mawaki Portable zai cigaba da kasancewa a hannun rundunar yayin da ake gaggauta shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban kotu.

Abin da ya jawo fadan Portable da Osupa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mawakan biyu na fada da juna ne kan zargin satar fasaha. Wannan rikicin ya sa Portable ya zagi Osupa a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu.

Wanda ya rera fitacciyar wakar “Zazu Zeh” ya kira mawaki Osupa mai shekaru 55 da sunaye marasa dadi, abin da ya tayar da kura a dandalin sada zumunta.

“Batun kudi ne ya haddasa rikicin,” in ji Portable, yana mai cewa, “na fusata ne saboda ina so in karbi kudina, sai na ji wai za su cire wakar.”

Portable ya janye hakurin da ya bayar

Portable ya fadi kalamai marasa dadi kan wani mawakin Fuji, lamarin da ya sa aka kama shi
'Yan sanda sun cafke mawaki Portable kan rigimarsa da wani mawakin Fuji. Hoto:@portblebaeby
Asali: Instagram

Bayan tarzomar jama’a, daga bisani Portable ya nemi gafarar Osupa a wani bidiyo da ya saki, yana rokon sa da cewa:

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

“Sarki Saheed Osupa, Baba na, don Allah ka yi hakuri. Ka dauke ni a matsayin yaro da kake koya wa tarbiyya.”

Yayin da yake nuna nadama, ya kuma ce rikicinsu wani salo ne na talla, yana mai cewa, “Muna tallata juna ne… don Allah ku bani dama in yi wasanni.”

Sai dai mawakin da aka haifa a Ogun wanda ke yawan jawo cece-kuce ,ya janye nadamar tasa bayan da aka ruwaito cewa Osupa ya nace cewa nadamar ba ta canza komai ba a kan batun.

'Yan sanda na neman Portable ruwa a jallo

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda sun ayyana fitaccen mawaki Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

An fara neman Portable ne bisa zargin kai hari ga jami’an gwamnati da ke bakin aiki a jihar, tare da wasu bata-gari da suka rufe fuska.

Rahotanni sun ce Portable da wasu mutum tara sun yi amfani da makamai wajen kai hari, inda suka raunata jami’an, sannan suka tsere suka kai rahoto wurin ‘yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel