Hadimin Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Tono Shirin Sanata Ndume kan Jam'iyyar APC

Hadimin Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Tono Shirin Sanata Ndume kan Jam'iyyar APC

  • Mai magana da yawun bakin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya sake taso Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a gaba
  • Daniel Bwala ya zargi Sanata Ali Ndume da zama maci amana ta hanyar yin tarurruka da 'ya 'yan jam'iyyar hamayya
  • Hadimin shugaban ƙasan ya nuna cewa Ndume zai shiga haɗakar ƴan adawa domin yanzu gangar jikinsa ce kawai ta rage a APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun bakin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya caccaki sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume.

Daniel Bwala ya zargi Sanata Ali Ndume da shirin shiga haɗakar jam’iyyun adawa.

Daniel Bwala da Ali Ndume
Daniel Bwala ya fadi shirin Ali Ndume kan APC Hoto: Bwala Daniel, Senator Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne a lokacin da ake hira da shi a shirin 'Sunday Politics' na tashar Channels Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndume da Bwala sun yi musayar yawu

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

A cikin ƴan kwanakin nan dai, Ndume da Bwala sun yi cacar baki da juna kan saɓanin ra’ayi a siyasa.

Sanata Ndume, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu suka kan manufofin Shugaba Bola Tinubu, ya nuna adawa da ƙudirin gyaran haraji da shugaban ƙasa ya turawa majalisar tarayya a shekarar 2024.

Haka kuma, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki saboda waɗannan kudirorin.

A yayin shirin, Bwala ya zargi Ndume da yi sauya sheƙa a baya, inda ya zargi sanatan da zama maci amana, ta hanyar yin taro da jam’iyyar adawa kafin daga bisani ya koma PDP.

A shekarar 2010, Ndume ya fice daga jam’iyyar ANPP zuwa PDP, yana mai bayyana rashin adalci a jam’iyyar a matsayin dalilin sauya sheƙarsa.

Me hadimin Tinubu ya ce kan Ndume?

"Bari na faɗa muku yau, kuma ina so kowa ya ji wannan, musamman shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje. Ruhi da zuciyar Sanata Ali Ndume suna tare da haɗakar jam’iyyun adawa, jikin shi kawai ya rage a cikin APC. Yana dab da barin jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Akwai wata a kasa: Kungiyar NCM ta gargadi 'yan Najeriya kan hadewar Atiku da El Rufai

"Ya yi hakan a baya lokacin da yake tare da Sanata kuma tsohon Gwamna Ali Modu Sheriff, lokacin da ya ji ba ya samun goyon baya."
"Haka ya koma PDP. Amma kafin ya sauya sheƙa, ya ci gaba da ganawa da su. A lokacin yana can yana aikin leƙen asiri."
Daniel Bwala ya soki Ali Ndume
Daniel Bwala ya ce Ndume zai shiga hadakar 'yan adawa Hoto: Bwala Daniel
Asali: Facebook
“Yana bayar da bayanai na sirri ga ɓangaren adawa. Dalilin da yasa nake cewa shugaban jam’iyya na ƙasa ya zama mai lura shi ne, domin yanzu haka Ndume yana tura saƙo ga waɗannan mutanen. Zai fi dacewa ya yi irin yadda El-Rufai ya yi."
“El-Rufai ya fito fili ya ce, ‘zan bar jam’iyya.’ Hakan ya fi mutunci da ƙima, domin bai tsaya a ciki yana aikin leƙen asiri ba. Ya fice kawai."
“Amma wannan (Ndume) yana ikirarin biyayya. Amma a wayonsa, yana tunanin, ‘Idan na zauna ina sukar jam’iyya daga ciki, mutane za su ce, wannan fa mamba ne na jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Abin ɓoye ya fito fili: Jerin sunayen Yarbawa 140 da Tinubu ya ba manyan muƙamai

- Daniel Bwala

Sanata Ndume ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya caccaki salon mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ndume ya yi zargin cewa shugaban ƙasan ya mayar da jiga-jigan APC waɗanda suka wahalta masa saniyar ware a gwamnatinsa.

Sanatan ya bayyana cewa rashin damawa da jiga-jigan na APC ne ya sanya wasu daga cikinsu suka fara ficewa daga jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng