Tsohon 'Dan Majalisa Ya Dauki Matakin Kotu da Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Baci a Ribas
- Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farah Dagogo, ya kalubalanci matakin gwamnatin tarayya na ayyana dokar ta baci a Ribas da kuma dakatar da 'yan majalisa
- Farah Dagogo ya shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Fatakwal, ya na kalubalantar yadda Bola Tinubu saboda dakatar da zababben gwamna
- Haka kuma, tsohon ɗan majalisar na tuhumar nadin da aka yi wa Ibok-Ete Ibas a matsayin mai kula da al’amuran jihar, yana cewa hakan ba ya da tushe a doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Farah Dagogo, tsohon ɗan majalisar wakilai, ya maka shugaban kasa Bola Tinubu da Ibok-Ete Ibas, da aka naɗa a matsayin mai kula da Ribas, a kotu kan dokar ta baci a jihar.
A karar da aka shigar gaban mai shari'a Adamu Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Fatakwal, an kalubalanci sahihancin dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar Ribas.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da kuma Ibok-Ete Ibas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 18 ga Maris, 2025, shugaban kasa Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar mai arzikin mai, yana mai bayyana cewa jihar na fama da rikicin siyasa mai tsawo.
An kalubalanci Tinubu kan dokar ta baci
Jaridar New Telegraph ta wallafa cewa a ranar Talata da ta gabata, lauyan Dagogo, C. I. Enweluzo, ya shigar da ƙarar neman a sada waɗanda ake ƙara takardun shari’a.
Mai shari’a Mohammed ya bayar da umarni cewa a lika takardun kotun a wuraren da aka sani cewa waɗanda ake ƙara ke zaune ta hanyar amfani da kamfanin isar da sakonni na DHL.
Mai shari’ar ya ce:
"An bayar da umarnin isar da takardun karar na asali da aka sanya kwanan wata 28 ga Maris, 2025, kuma aka shigar ranar 2 ga Afrilu, 2025, da sauran takardun da ke tare da su da kuma wadanda za su biyo baya, ga wadanda ake ƙara ta hanyar aika su ta DHL zuwa wuraren da aka sani na karshe da suke zama."
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga Mayu domin ci gaba da gabatar da hujjoji a kan shari'ar kalubalantar hurumin gwamnatin tarayya na sa dokar ta baci a Ribas.
Abin da ake kalubalantar Tiubu a kai
Hon. Dagogo ya ce ayyana dokar ta baci tare da dakatar da gwamnan jihar, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas na tsawon watanni shida ya saba wa dokar kasa.

Asali: Instagram
Haka kuma, Farah Dagogo yana kalubalantar nadin da shugaban kasa Tinubu ya yi wa Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan rundunar ruwa, a matsayin mai kula da jihar Ribas.

Kara karanta wannan
"Ka yi hattara da El-Rufa'i,' Jagora a APC ya shawarci Atiku kan takarar shugaban kasa
Ribas: Gwamnoni sun maka Tinubu a kotu
A baya, kun samu labarin cewa gwamnonin PDP 11 sun shigar da ƙara a gaban Kotun Koli domin kalubalantar ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers.
An shigar da karar mai lamba SC/CV/329/2025 daga gwamnonin jihohin Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Plateau, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa don neman 'yancin Ribas.
Karar na zuwa a lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan halaccin matakin da shugaban kasa Tinubu ya ɗauka kan jihar Rivers, inda ya dakatar da duka shugabannin zartarwa da na majalisa na jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng