Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Ainihin Abin da Ya Kai Bola Tinubu Faransa
- Fadar shugaban kasa ta bayyana rashin jin daɗin yadda ake baza labarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya tafi Faransa domin a duba lafiyarsa
- Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin bayanan da ake yadawa
- Fitaccen mai kare haƙƙin ɗan Adam kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, ne ya yi zargin cewa Tinubu ya tafi kasar Faransa ne domin ganin likita
- Sai dai Bwala ya ce akwai alamun da ke nuna cewa lafiyar Tinubu ƙalau, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da ganin ayyukansa a kasar da ya tafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasar Faransa domin ganin likita.
Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan inda ya kira zargin a matsayin tsagwaron karya..

Asali: Twitter
Channels TV ta ruwaito cewa Bwala yana mayar da martani ne ga ikirarin da fitaccen mai rajin kare hakkin dan Adam kuma dan siyasa, Omoyele Sowore.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sowore, ya bayyana cewa tafiyar shugaban kasa zuwa Faransa na da nasaba da neman kulawar likita domin a duba lafiyarsa.
Sowore ya fusata kan tafiyar Tinubu Faransa
Jaridar Punch ta wallafa cewa tun da fari mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya cikin makonni biyu.
Amma Sowore ya yi zargin cewa labarin ba haka ya ke ba, tare da kafe wa a kan cewa shugaban kasar ya tafi neman lafiya ne.

Asali: Facebook
Sowore ya rubuta cewa:
"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake tserewa daga Najeriya zuwa Faransa domin neman lafiyar, kodayake wasu ma’aikatan ofishinsa da suka saba da karya suna cewa tafiyar aiki ce."

Kara karanta wannan
"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari
"Abin takaici ne ganin yadda kimanin ‘yan Najeriya miliyan 200 ke ci gaba da kasancewa cikin duhu, suna karbar bayanan karya kullum ba tare da sun dauki matakin kubutar da kansu daga wannan hali ba."
“Aiki Tinubu ya tafi Faransa,” Bwala
Da yake mayar da martani, Bwala ya kare shugaban kasarsa inda ya ce babu ko kadan na gaskiya a zargin da ake yi.
Ya ce:
"Tafiye tafiyen shugaban kasa zuwa Faransa ba su da nasaba da rashin lafiya. Ba ku ga yadda ake kai masa ziyara ba? Wato ana samun rahotanni a kai a kai na yadda mutane ke ganinsa."
"Shugaban kasa bai je ganin likita ba. Tafiyar aiki ce, kuma muna wallafa ayyukansa tun lokacin da ya isa."
Shugaba Bola Tinubu ya tafi Faransa
A wani labarin, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tashi zuwa birnin Paris na kasar Faransa a domin wata gajeriyar ziyarar aiki ta mako biyu.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya kuma ya ce tafiyar za ta ba Tinubu damar waiwaye kan ayyukansa.
Onanuga ya kara da cewa shugaban kasar zai kuma tantance nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki da shirin daukar matakai na gaba wajen tafi da Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng