Ana Jimamin Kisan kusan Mutum 50, an Sake Sabon Ta'addanci a Plateau

Ana Jimamin Kisan kusan Mutum 50, an Sake Sabon Ta'addanci a Plateau

  • An sake samun sabon ta'addanci kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Plateau da ke yankin Arewacin Najeriya
  • Wasu mutane da ba a bayyana ko su waye ba sun shiga har cikin gida sun hallaka wasu mutum uku a ƙaramar hukumar Bassa
  • Kisan mutanen guda uku ƴan gida ɗaya na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jimamin kashe wasu aƙalla mutane 50 a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - An sake aikata ta'addanci a jihar Plateau yayin da ake jimamin kisan da aka yi wa mutane a ƙaramar hukumar Bokkos.

Lamarin ya auku ne bayan an kashe wani uba tare da ƴaƴansa biyu a ƙauyen Zogu da ke yankin Miango, a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau.

An kashe mutane a Plateau
An kashe mutane uku a Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mai magana da yawun ƙungiyar Irigwe Development Association (IDA), Sam Jugo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jos.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon ɗan wasa kuma Kocin Super Eagles ya rasu a shekara 74

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi sabuwar ta'asa a Plateau

Sam Jugor ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Weyi Gebeh (mai shekara 56), Zhu Weyi (mai shekara 25), da Henry Weyi (mai shekara 16).

A cewar Sam Jugo, an kashe waɗannan mutane ne da daddare a lokacin da suke barci, ya bayyana wannan harin da cewa aiki ne na dabbanci da rashin imani.

"Shugabancin ƙungiyar Irigwe Development Association (IDA) ya samu labarin wani sabon hari da aka kai wa ƙauyen Zogu da ke Miango."
"Harin ya yi sanadiyyar mutuwar uba da ƴaƴansa guda biyu, masu suna Weyi Gebeh, mai shekara 56, Zhu Weyi, mai shekara 25, da Henry Weyi, mai shekara 16.
“Wannan lamari ya kawo jimillar mutuwar mutane tara a makon nan kawai. IDA na bayyana matuƙar damuwarta bisa yadda halin tsaro ke ƙara tabarbarewa a yankin Irigwe."
"Ƙungiyar na kiran hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace domin kawo ƙarshen wannan ta’addanci da kuma cafke masu laifi domin su fuskanci hukunci."

Kara karanta wannan

Yadda darektan APC ya yi wani irin mutuwa a hannun ƴan bindiga a Abuja

An kai hari a Plateau
Miyagu sun kashe mutane a Plateau Hoto: @PoliceNG
Asali: Getty Images
"Yadda waɗannan miyagu ke kutsawa ƙasarmu suna kashe mutane ba tare da jin tsoron hukuma ba, na nuni da cewa akwai wata mummunar manufa da ke ɓoye fiye da ramuwar gayya kawai."
“Saboda haka, IDA na kira ga gwamnatin jihar Plateau da hukumomin tsaro da su yi duk abin da ya dace don kawo ƙarshen kisan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a ƙasar Irigwe."

- Sam Jugo

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a samu martani daga mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, da kuma na rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred ba.

Gwamnan Plateau ya faɗi masu ɗaukar nauyin ta'addanci

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya yi magana kan hare-haren ta'addancin da ake kai wa a jihar.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa akwai masu ɗaukar nauyin hare-haren ta'addancin da ake kai wa kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Caleb Mutfwang ya nuna cewa wasu ƙungiyoyin ƴan ta'adda ne ke kai hare-haren da nufin yin kisan ƙare dangi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng