Abba Ya Biya Bashin Sama da ₦2bn na Daliban da Ganduje Ya Yi Watsi da Su

Abba Ya Biya Bashin Sama da ₦2bn na Daliban da Ganduje Ya Yi Watsi da Su

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ta kammala biyan wani tsohon bashin ₦2.5bn da jami’ar Cyprus ke bin gwamnatin tun a zamanin Abdullahi Ganduje
  • Wannan kudin ya kasance ragowar bashin kudin makaranta na ɗalibai da gwamnati ta dauki nauyin karatunsu, wanda suka kammala shekaru biyar baya
  • Yanzu haka, bayan shafe zaman gida babu makoma, daliban su akalla 84 za su samu damar karbar takardun shaidar kammala karatu a fannoni daban daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoGwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir Yusuf, ya kammala biyan bashin da ya kai €1.4m, wato kimanin ₦2.5bn da ake bin jihar a jami’ar Near East da ke ƙasar Cyprus.

Wannan kuɗi ya ƙunshi kudin makaranta na ɗalibai 84 da suka yi karatu a fannin lafiya da kimiyyar lafiya waɗanda suka kammala karatu tun 2016.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa: Halin da ake ciki bayan wakilan gwamnatin Kano sun isa Edo

Gwamna
Gwamnati ta biya kuɗin dalibai 84 a Cyprus Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

NNPP Kwakwasiyya ta wallafa a Facebook cewa daliban ba su karɓi takardun shaidar kammala karatu ba saboda bashin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ki biya masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cyprus: Za a ba daliban Kano shaidar karatu

A cikin sanarwar da Mai ba gwamna shawara ta musamman kan harkokin watsa labarai, Ibrahim Adam, ya fitar, wacce Legit ta samu gani a yammacin Lahadi, an ce daliban Kano za su karbi takardun kammala karatu.

A cewar Ibrahim Adam a shafin Facebook, nan ba da daɗewa ba za a mika takardun shaidar waɗannan ɗalibai zuwa hukumar tallafin karatu ta Jihar Kano ta hannun jakadan Najeriya a Turkiyya.

Wannan mataki zai kawo ƙarshen wata matsala da ta dade tana damun ɗaliban tun bayan kammala karatunsu, inda aka bar su babu kyakkyawar makoma a bokon da suka yi.

A yayin da yake jawabi a taron majalisar zartarwa ta jihar Kano karo na 22, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana jin daɗinsa kan yadda lamarin ya kaya.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

Ya ce:

“Na ji daɗin jagorantar zaman majalisar zartarwa ta jihar karo na 22 yau. Wannan zama ya ba ni damar sanar majalisa cewa mun yi nasarar sauke bashin kudin makaranta da ake bin jihar Kano zuwa kasa da ₦2bn daga ainihin abin da ake bin mu a jami’ar Near East da ke Cyprus.”

suka ɗauka ba wai kawai warware matsala ce ba, har ma ya ceci jihar Kano wajen sauke mata nauyi.

Abba: 'Gwamnatin Ganduje ta tarawa Kano bashi'

A cewar gwamnan, asalin bashin ya kai fiye da €3m, kimanin ₦4bn, wanda aka tara daga shekarar 2015 zuwa 2019 a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata.

Ziyarar da Gwamna Yusuf ya kai ƙasar Cyprus ta bayyana cewa ɗaliban da abin ya shafa sun dawo gida tun fiye da shekaru biyar da suka wuce ba tare da takardun karatunsu ba.

Gwamna
Gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai waɗanda suka kammala digiri na biyu a fannin likitanci da wasu manyan fannoni.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Gwamna Yusuf ya nuna damuwa da halin da waɗannan matasa suka shiga, yana mai cewa rashin samun takardunsu ya hana su cigaba da sana’ar da suka koya.

Yadda gwamnan Kano ya biya kudin daliban

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara ƙasar Cyprus a ranar 9 ga Disamba, 2024, inda ya gana da shugabannin jami’ar Near East.

A lokacin wannan ganawa ne suka cimma matsaya kan yadda za a biya ragowar kudin da gwamnatin Kano ke bin jami’ar.

Kisan Uromi: Gwamnan Kano na son ayi adalci

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jin dadin mayakan da gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya dauka bayan kisan mafarautan jiharsa a Uromi.

A cewar wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Gwamna Abba ya bayyana cewa ita ma gwamnatin tarayya ta yi abin da ya dace zuwa yanzu.

Sai dai ya mika bukatarsa, yana neman a gaggauta fito da wadanda aka tabbatar suna da hannu a cikin babbake Kanawa da suka ratsa ta Uromi a jihar Edo bai tare da laifin komai ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng