'Ka Gwada Zuwa Borno Ka Gani': Jigon APC Ya Kalubalanci Ministan Tinubu kan Boko Haram

'Ka Gwada Zuwa Borno Ka Gani': Jigon APC Ya Kalubalanci Ministan Tinubu kan Boko Haram

  • Wani jigo a APC, Yerima Lawan Kareto, ya bukaci Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya kai ziyara wuraren da Boko Haram ke da iko
  • Hon. Yerima Lawan Kareto ya ce zai raka ministan tarayyan har zuwa Damasak domin ya ga da idonsa yadda al’amarin ya tabarbare a Borno
  • Gwamna Babangana Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda sojoji ke rasa iko a wurare da dama, duk da kokarin gwamnati na yaki da ta’addanci
  • Tsohin kwamishinan ya ce maganar da hadimin minista ya fitar ba za ta kwantar da hankalin mutanen Borno ba, sai an kai ziyara da yafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Yerima Lawan Kareto, ya kalubalanci Ministan yada labarai, Mohammed Idris kan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon ɗan wasa kuma Kocin Super Eagles ya rasu a shekara 74

Kareto ya kalubalanci ministan da ya gwada zuwa yankunan da Boko Haram ke iko da su a jihar Borno.

An kalubalanci ministan Tinubu kan Boko Haram
Jigon APC a Borno ya fadawa Ministan Tinubu gaskiya kan Boko Haram. Hoto: Ministry of Information.
Asali: Twitter

Kareto, wanda tsohon Kwamishina ne ya ce zai raka ministan da kansa zuwa yankin domin ya ga gaskiyar halin da ake ciki, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya damu da hare-haren Boko Haram

Gwamna Babagana Zulum ya bayyana damuwarsa a wani taron tsaro yana mai cewa dakarun soja suna rasa mafaka a wasu sassa na jihar.

‘Yan Boko Haram sun kwace wuraren soja a Wulgo, Sabon Gari, Wajirko, Izge da wasu garuruwa da ke cikin jihar Borno.

Martanin minista kan matsalar Boko Haram

Ministan ya saba da ikirarin Gwamna Zulum inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram wajen yaki da ta’addanci da ‘yan bindiga.

Ya ce jami’an tsaro na aiki babu kakkautawa domin dawo da daidaito a Borno da sauran jihohin da rikici ya shafa a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yadda darektan APC ya yi wani irin mutuwa a hannun ƴan bindiga a Abuja

Sai dai hadimin ministan, Rabiu Ibrahim, ya ce rahoton da aka alakanta da ministan ba gaskiya ba ne, ya ce:

"Ba gaskiya ba ne kuma an karkatar da kalamansa, a yi watsi da Zulum, Boko Haram ba ta kwace Borno ba, kamar yadda ake yadawa."
Jigon APC ya fadi halin yankunan Borno ke ciki kan Boko Haram
Jigon APC a Borno ya soki ministan Tinubu kan hare-haren Boko Haram. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

Jigon APC ya kalubalanci ministan Tinubu

Amma Kareto ya ce maganar da hadimin ministan ya fitar ba za ta kwantar da hankalin mutanen Borno ba har sai an kai ziyara tare da neman yafiya.

Ya ce:

“Ina sanar da minista cewa wannan jawabi ba zai rage radadin da mutanen Borno ke ji ba, musamman masu yarda da Gwamna Zulum.
“Ministan labarai, Idris ya kamata ya zo Borno a karkashin gayyata ta, mu tafi tare zuwa Damasak domin ya ba da hakuri kuma ya fadi gaskiya.”

Kareto ya ce mutanen Borno na tare da gwamnatin, ya kuma bukaci Gwamna Zulum da dakarun da su ci gaba da jajircewa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

Rundunar tsaro ta yi martani ga Zulum

A wani labarin, an ji rundunar tsaro ta yi martani ga Babagana Umara Zulum bayan sun samu sabani kan sake bayyanan hare-haren Boko Haram a jihar Borno.

Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda 'yan ta'adda ke kai farmaki sansanonin sojoji, ana kashe mutane da sace-sace a yankuna.

A martaninsta, rundunar ta ce jami’an tsaro na aiki tukuru wajen dawo da zaman lafiya a jihar da ma fadin kasar baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng