Lokaci Ya Yi: Tsohon 'Dan Wasa kuma Kocin Super Eagles Ya Rasu a Shekara 74
- Tsohon kyaftin din Super Eagles kuma mai horas da ƙungiyar, Christian Chukwu, ya rasu yana da shekaru 74, abin da ya girgiza Najeriya
- Tsohon dan wasa, Olusegun Odegbami ya bayyana bakin ciki bisa rasuwar abokinsa,ya ce Chukwu babban gwarzo ne a tarihin ƙwallo
- Chukwu ya jagoranci Green Eagles suka lashe kofin nahiyar Afirka a 1980, kuma ya kai Super Eagles wasan kusa da na ƙarshe a 2004
- A 2021, jita-jitar mutuwarsa ta yadu, sai dai ya karyata hakan yayin da rasuwar a wannan lokaci ta kawo ƙarshen wani tarihi a kwallon ƙafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Tsohon kyaftin na Green Eagles da kuma mai horas da Super Eagles, Christian Chukwu, ya rasu.
An sanar da rasuwar marigayin a yau Asabar yana da shekaru 74 duk da cewa ba a bayyana dalilin mutuwar ba.

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Asali: Getty Images
Tsohon dan wasan Super Eagles ya rasu
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai cike da tausayawa da tsohon ɗan wasa kuma fitaccen gwarzo, Dr. Olusegun Odegbami ya fitar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Odegbami ya bayyana alhininsa kan babban rashi da al'ummar Najeriya suka yi dama masu sha'awar kwallon kafa.
Ya ce:
“Na samu labarin cewa tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau Asabar, Christian Chukwu abokina na kusa kuma abokin wasana, ɗaya daga cikin manyan ‘yan wasa a tarihin ƙwallon Najeriya ya rasu.
"Tsohon kyaftin da mai horar da ƙungiyar ƙasa, ya rasu. Babuje, Emmanuel Okala, MON, ne ya faɗa mani wannan labari mai ban tausayi da ‘yan mintoci kaɗan da suka wuce!.
"Allah ya ba ‘Onyim’ gida a Aljanna, kuma ya ba iyalansa haƙurin wannan babban rashi da aka yi."

Asali: Getty Images
Gudunmawar marigayin a harkar ga Super Eagles
An ce Chukwu ya kasance ginshiƙi a ƙwallon ƙafa ta Najeriya, inda ya taka rawa sosai a fili da wajen fili tare da ba da gudunmawa mai tsoka a harkar wasanni..
Ya jagoranci Green Eagles zuwa nasarar lashe kofin Afirka a 1980, sannan ya horas da ƙungiyar ƙasa har suka kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar AFCON ta 2004, The Nation ta ruwaito.
A shekarar 2021, jita-jitar mutuwarsa ta karade duniya, wanda ya sa ya fito fili ya karyata hakan yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 70.
Rasuwarsa alama ce ta ƙarewar wani babi mai muhimmanci a tarihin ƙwallon ƙafa ta Najeriya, yayin da sakonnin ta’aziya ke ci gaba da shigowa daga ko’ina cikin duniya.
Legit Hausa ta tattauna da masoyin kwallon kafa
Wani tsohon mai sha'awar kallon kwallon Najeriya ya kaɗu da samun labarin rasuwar Christian Chukwu.
Farouk Usman ya ce tabbas 'Chairman' kamar yadda kiransa ya taka rawar gani matuka.
"Ba zan manta irin gudunmawar da ya bayar ba musamman lokacin da yake kyaftin din 'Green Eagles'."
- Cewar Farouk
Manchester ta dawo zawarcin tauraron S/Eagles
Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun ce Napoli da Manchester United na tattaunawa kan siyan Victor Osimhen, yayin da kungiyarsa ke shirin rage farashinsa.
Cinikiyyar Napoli da United ta kara karfi yayin da kungiyar ta ki yarda ta sayar da Osimhen ga Juventus saboda gudun karfafa abokan hamayya a Italiya.
Sai dai Manchester United ta dauki Osimhen a matsayin babban burinta, duk da rashin tabbas na shiga gasar Turai yayin da Arsenal ma ke muradinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng