Atiku, El Rufa'i, Pantami da Manyan 'Yan Adawa Sun Gana da Buhari a Kaduna

Atiku, El Rufa'i, Pantami da Manyan 'Yan Adawa Sun Gana da Buhari a Kaduna

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna bayan hutu
  • Ya jagoranci manyan mutane ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal zuwa gidan Buhari
  • Sheikh Isa Ali Pantami da Abubakar Malami su ma sun kai ziyarar Sallah ga tsohon shugaban, suna addu’ar Allah ya karbi ibadar da aka yi a Ramadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar gaisuwar Sallah a gidansa da ke Kaduna.

Atiku Abubakar ya ce kai ziyayar ne bayan ya kammala gudanar da bikin Sallah a Yola a matsayin Waziri Adamawa.

Buhari
Atiku da wasu manyan 'yan siyasa sun ziyarci Buhari. Hoto: Paul O Ibe
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a cikin wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Atiku ya ziyarci Buhari bayan Sallah?

Atiku ya ce jagorancin da ya ke yi a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin gargajiya a Adamawa ne ya hana shi kai gaisuwar Sallah ga Buhari a lokacin bukukuwan Sallah.

Yayin da aka yi bikin sallah a Yola, Atiku ya ce ya yi bikin tare Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Musdafa.

Sai dai a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, Atiku ya samu damar kai ziyarar tare da rakiyar wasu fitattun shugabannin siyasa domin gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Fitattun 'yan siyasa sun raka Atiku zuwa Kaduna

Atiku ya jagoranci tawagar da ta hada da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal zuwa gidan Buhari da ke Kaduna.

Baya ga haka an hango wasu manyan jagororin jam'iyyar SDP da El-Rufa'i ya koma a kwanakin baya cikin tawagar.

Kara karanta wannan

Bayan mako 1 yana shiru, Buhari ya magantu kan rasuwar Idris Dutsen Tanshi

Mutane suna ganin ziyarar ta nuna girmamawa da kuma ci gaba da tuntubar juna tsakanin tsofaffin shugabannin Najeriya, musamman bayan kammala babban bikin Sallah.

Sai dai an fara ce-ce-ku-ce kan ziyayar kasancewar wasu sun fara ba ta fassarar shirin siyasar 2027.

Pantami da Malami sun ziyarci Buhari

A gefe guda kuwa, tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana a shafinsa na X cewa shi da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN, CON), sun ziyarci Buhari.

Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa sun kai gaisuwar Sallah ga Buhari a ranar Juma’a a gidansa na Kaduna.

Pantami ya ce:

“Mun kai gaisuwar Sallah ga Baba Buhari tare da Abubakar Malami a yau. Allah ya karɓi ibadunmu na Ramadan da bayan sa.”

Shehu Sani ya yi wa Buhari raddi

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi raddi wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zariya da wani magidanci ya kashe ɗan uwansa da duka

Raddin Shehu Sani ya zo ne a daidai lokacin da Buhari ya ce ya kammala mulki amma bai tara kudin gwamnati ba.

A martanin da ya yi, Sanatan ya ce Allah ne kadai ya san gaskiyar maganar Buhari kuma babban abu da ya fi dacewa shi ne ko mulkinsa ya amfani talaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng