Najeriya Ta Hada Kai da Kasar Japan domin Tallafawa Manoma 500,000
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta yi hadin gwiwa da JICA don tallafawa manoma 500,000 kafin daminar 2025
- Gwamnatin tarayya ta ce za a yi amfani da tallafin kudi wajen samar da kayan aiki, kula da amfanin gona da dai sauransu
- Bayanan da gwamnatin Najeriya ta fitar sun nuna cewa manufar shirin ita ce samar da isasshen abinci da inganta rayuwar manoma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dauki sabon mataki domin karfafa samar da abinci da bunkasa tattalin arzikin karkara.
Najeriya za ta tabbatar da haka ne ta hanyar hadaka da Hukumar Hadin Gwiwar Kasar Japan (JICA).

Asali: Twitter
A wani rahoto da ma'aikatar yada labarai ta wallafa a shafinta, an ce za a tallafa wa manoma 500,000 kafin fara damunar shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin da ke karkashin tallafin gaggawa na JICA don samar da abinci mai darajar Yen biliyan 12, ya kunshi samar da kayayyakin noma a kan lokaci da kula da amfanin gona bayan girbi.
Ministan Kudi, Wale Edun, tare da Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari da Shugaban Bankin Noma, Ayo Sotinrin, sun gana da wakilan JICA a Abuja domin tsara yadda za a aiwatar da shirin.
Za a bai wa manoma tallafin kayan aiki
A yayin ganawar, an bayyana cewa JICA za ta tallafa wajen samar da kayan aiki ga manoma 500,000 kafin damunar shekara mai zuwa.
An bayyana cewa matakin zai taimaka wajen fara noman damina da wuri tare da inganta yadda ake girbin amfanin gona.
Bayan haka, za a inganta yadda ake adana amfanin gona bayan girbi da kuma saukaka hanyoyin da manoma za su sayar da kayan amfaninsu cikin sauki da riba mai yawa.
Shirin JICA zai inganta rayuwar manoma
Shugabanni sun bayyana cewa hadin gwiwar da aka kulla da JICA wata dama ce da za ta taimaka wajen inganta tsarin noma a Najeriya.
Za ta kara yawan amfanin gona, rage radadin yunwa da kuma kara habaka tattalin arzikin manoma a karkara.
Shirin na daya daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na sake fasalta tsarin abinci da tabbatar da dorewar samar da abinci mai yawa duk da kalubalen da duniya ke fuskanta na sauyin yanayi.
Shirin gwamnatin Najeriya na habaka tattali
Daraktan Yada Labaran Ma’aikatar Kudi, Mohammed Manga, ya ce gwamnatin na da yakinin cewa hadin gwiwa da Japan zai taimaka wajen samun wadataccen abinci a Najeriya.
Baya ga haka, Mohammed Manga ya kara da cewa za a samu habakar tattalin arziki mai dorewa a karkashin shirin.
Shirin zai kuma bai wa matasa da mata masu yawa damar shiga harkar noma domin samun riba da dogaro da kai.

Kara karanta wannan
Farashin man fetur zai ƙara araha a Najeriya da Gwamnatin Tinubu ta dawo da tsarinta

Asali: Getty Images
Gwamnati za ta kawo tallafin kasuwanci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fitar da wani shiri na musamman domin tallafawa al'umma.
Ministan ilimin Najeriya ne ya bayyana matakin da gwamnatin ta dauka inda ya ce za a ware Naira bliyan 300 domin tabbatar da shirin.
Ana sa ran cewa shirin zai mayar da hankali ga matasan da suka kammala makaranta domin a karfafe su, su dogara da kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng