Abin da Aka Fadi ga Tinubu, Matawalle bayan Aika Rikakken Ɗan Ta'adda Lahira a Zamfara

Abin da Aka Fadi ga Tinubu, Matawalle bayan Aika Rikakken Ɗan Ta'adda Lahira a Zamfara

  • Al’ummar Anka a Zamfara sun yaba wa Bola Tinubu, Bello Matawalle da Janar Christopher Musa kan hallaka shugaban ‘yan bindiga Mati
  • Shugaban al’ummar Anka, Muhammed Usman, ya gode wa Matawalle bisa taimakon sojoji wajen farmakin da ya hallaka ‘yan bindigar
  • An ce sojojin sun gudanar da farmakin ne a karkashin "Operation Munzo", suka kwato makamai da lalata sansanonin 'yan bindiga a yankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Wasu mazauna karamar hukumar Anka a jihar Zamfara sun yaba wa Shugaba Bola Tinubu da Minista Bello Matawalle.

'Yan yankin sun kuma jinjinawa hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa bayan aika shahararren dan bindiga lahira.

An yabawa Matawalle da Tinubu kan kakkabe ƴan bindiga
Al'ummar Anka a Zamfara sun jinjinawa Matawalle da Tinubu bayan hallaka ɗan bindiga, Mati. Hoto: Dr. Bello Matawalle, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yaƙi da Ta'addanci: An yabawa Matawalle, Tinubu

Shugaban al’ummar Anka, Muhammed Usman Anka, ya fitar da jawabi yana godiya ga Minista Matawalle saboda irin gudummawar da ya bayarwa, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al'ummar yankin sun yi wannan godiya ne bayan kakkabe wani hatsabibin ɗan ta’adda, Mati, da yaransa a wani samame da gwamnatin tarayya ta dauki nauyi.

Wannan farmaki na cikin shirin yaki da rashin tsaro a Arewa maso Yamma inda aka kwato makamai da rushe sansanin ‘yan ta’adda.

A cewar jawabin, an kaddamar da farmakin ne karkashin shirin gwamnati mai suna “Operation Munzo” domin dawo da zaman lafiya a Zamfara.

An yabawa Matawalle kan yaki da ta'addanci a Najeriya
Mazauna yankin Anka a Zamfara sun jinjinawa Matawalle da Tinubu bayan kisan ɗan bindiga, Mati. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Yadda sojoji suke yakar ta'addanci a Arewa

Sojoji sun soma ne daga Bagega a Anka suka ci gaba zuwa Tibuki da Sabuwar Tunga kafin su kai hari sansanin Mati

An bayyana fafatawar da aka yi da cewa mai tsauri ce inda aka samu nasarar kashe Mati da manyan kwamandojinsa a artabu.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindiga PKT, AK-47 guda biyar, harsasai 487, na’urorin sadarwa da kayan sojoji da ‘yan sanda.

Sojojin sun lalata babura uku da ‘yan bindigar ke amfani da su sannan sun kwato shanu da suka sace a yankin.

Kara karanta wannan

Turji ya sauya salo, an gano ƴan ta'adda na shiga Sokoto daga dazukan Zamfara

A halin yanzu, sojojin na ci gaba da bincike a dazukan yankin domin kamo sauran miyagun da suka rage a maboyarsu.

Matawalle ya yabawa ƙoƙarin sojojin Najeriya

A ɓangarensa, Minista Matawalle ya jinjinawa jarumtar sojoji kan jajircewar da suke nunawa a yaƙi da ta'addanci inda ya ce:

“Operation Munzo wani bangare ne na shirin murkushe ‘yan ta’adda baki daya.”
"Kwanakin wadannan miyagu sun ƙare. Shugaba Tinubu ya ba da umarnin murkushe su gaba daya.”

Ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar tsaro za ta ci gaba da tallafawa dakarun Najeriya wajen tabbatar da tsaro a yankin.

Yan bindiga sun kai hari a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa ƴan bindiga na ci gaba da kai hare-hare bayan kisan da jami'an tsaro suka yi wa wasu daga cikin manyan jagororinsu a jihar Zamfara.

Tsagerun sun ƙaddamar da hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Tsafe domin yin ramuwar gayya.

An ce hare-haren na ƴan bindiga sun jawo asarar rayuka yayin da aka sace mutane sama da 60 zuwa cikin daji a 'yan kwanakin nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng