Bayan Fara Tambayoyi, Gwamnatin Kano Ta Tura Tawaga Zuwa Edo da Aka Hallaka Hausawa

Bayan Fara Tambayoyi, Gwamnatin Kano Ta Tura Tawaga Zuwa Edo da Aka Hallaka Hausawa

  • Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci kwamiti zuwa jihar Edo domin binciken kashe-kashen da suka faru a kauyen Uromi
  • Rahotanni sun ce lamarin ya ta da hankulan jama’a, musamman ‘yan asalin Kano da ke zaune a yankin da abin ya shafa
  • Kwamiti ya kunshi manyan jami’ai ciki har da Sarkin Rano, da kwamishinoni daga ma’aikatun addini, kananan hukumomi, da harkokin mata
  • Gwarzo ya ce sun tafi Edo domin tattaunawa da gwamnati, jami’an tsaro, da sarakunan gargajiya domin samar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamiti mai karfi kan kisan Hausawa da aka yi a jihar Edo.

An kafa kwamitin karkashin jagorancin mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo domin binciken kashe-kashen da suka faru a Uromi.

Kara karanta wannan

Bayan zuwan tawagar Kano, Okpebholo ya fadi yadda tinubu ya ji kan kisan ƴan Arewa

Gwamnatin Kano ta dura a Edo bayan kisan Hausawa
Mataimakin gwamnan Kano ya jagoranci tawaga zuwa Edo bayan kisan ƴan Arewa. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, HE. Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Twitter

Wannan na cikin wata sanarwa da hadimin Gwarzo a ɓangaren yada labarai, Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Edo ya jajantawa gwamnatin Kano

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya je jihar Kano domin jajanta wa Gwamna Abba Kabir da iyalan mutane 16 da aka kashe a Uromi.

Okpebholo ya kai wannan ziyara ta musamman ne domin nuna alhinin abin da ya faru da mutanen da aka kashe a karshen watan Maris.

Majiyoyi sun ce Gwamnan Edo ya gana da Abba Kabir a gidan gwamnati domin jajanta masa da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Tawagar gwamnatin Kano ta isa Edo kan kisan Hausawa
Mataimakin gwamnan Kano ya jagoranci tawaga zuwa Edo game da kisan ƴan Arewa. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Twitter

Musabbabin kafa kwamitin bayan kisan Hausawa

Ibrahim Garba ya ce an kafa kwamitin ne domin bincike da kuma kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

Kwamiti ya hada da Sarkin Rano, Ambasada Mohammad Isa Umar, da kwamishinoni.

Sauran sun hada da kwamishinonin addini, kananan hukumomi, ayyuka na musamman da harkokin mata, da shugaban karamar hukumar Bunkure.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Ya bayyana cewa gwamnati ta kafa wannan kwamiti ne saboda yadda mutane suka nuna bacin rai da damuwa kan kashe-kashen da suka faru a Uromi.

A filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano kafin tafiya, Gwarzo ya bayyana cewa kwamiti zai tabbatar da adalci, zaman lafiya da sulhu tsakanin al’ummar yankin.

Gwarzo ya ce:

“Aikinmu a bayyane yake, za mu yi bincike, tuntuba da bayar da shawarwari na magance matsaloli.
"Kuma wannan ba wai bincike kadai ba ne, aikin wanzar da zaman lafiya ne."

Gwarzo ya ce za su gana da gwamnan Edo, shugabannin tsaro, sarakunan gargajiya da kungiyoyin farar hula domin tattaunawa da neman mafita mai dorewa.

Majalisa za ta sauya fasalin aikin sa-kai

Kun ji cewa Kwamitin Sojin ƙasa na Majalisar Wakilai ya yi kira da a bayar da horo da kuma sanya ido kan ƙungiyoyin 'yan banga a Najeriya.

Wannan ya biyo bayan kisan wasu 'yan Arewa 16 da aka yi a Uromi, jihar Edo, wanda ya ta da kura a faɗin ƙasa.

Hon. Babajimi Benson ya ce wajibi a kafa ‘yan sandan jihohi domin rage nauyin da ke kan sojoji da kuma inganta tsaro a matakin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng