Gwamna Ya Yi Alhini da Allah Ya Karbi Rayuwar Ɗan Majalisa, Hon. Kasuwar Daji

Gwamna Ya Yi Alhini da Allah Ya Karbi Rayuwar Ɗan Majalisa, Hon. Kasuwar Daji

  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya yi alhinin rasuwar Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar Kaura Namoda ta Kudu
  • A wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis, 10 ga watan Afrilu, 2025, Gwamna Dauda ya yi addu'ar Allah Ya jiƙan marigayin, ya ba iyalansa hakuri
  • Rahotanni sun nuna cewa an yi jana'izar ɗan Majalisar Dokokin Zamfara, Hon Aminu Kasuwar Daji jiya Laraba bisa tsarin addinin musulunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal ya bayyana jimami kan rasuwar ɗaya daga cikin mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara.

Gwamna Dauda Lawal, ya yi alhini da jajantawa dangin marigayi, Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara da daukacin al’ummar jihar bisa rasuwar Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji.

Hon Aminu Kasuwar Daji da Gwamna Dauda.
Gwamna Dauda Lawal ya yi ta'aziyyar rasuwar ɗan Majalisar Dokokin Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Saƙon ta'aziyyar mai girma gwamnan na kunshe ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter yau Alhamis, 10 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan Majalisar Dokokin Zamfara ya rasu

Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji mai wakiltar Kauran Namoda ta Kudu a Majalisar Dokokin jihar Zamfara ya rasu ne jiya Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025.

Duk da babu cikakken bayani kan rasuwarsa, amma rahotanni sun nuna cewa an yi wa marigayin sallar jana'iza jiya Laraba kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Tuni dai manyan mutane da magoya baya suka fara alhini da zuwa ta'aziyyar Marigayi Hon. Aminu Kasuwar Daji.

Sanata Sahabi ya yi alhinin rashin Ɗan Majalisar

Sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Ya'u Sahabi na ɗaya daga cikin waɗanda suka yi alhinin rashin ɗan Majalisar.

A cewar Sanata Sahabi, Aminu Kasuwar Daji mutum ne da tawali’u da gaskiya suka mamaye rayuwarsa, inda hakan ya zama abin koyi ga mutane.

Da yake alhinin wannan rashi, Gwamna Dauda Lawal ya yi addu'ar Allah Ya jiƙan ɗan Majalisar kuma ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

An shiga alhini bayan ɗan majalisa mai ci a Zamfara ya riga mu gidan gaskiya

Dauda Lawal.
Gwamna Dauda Lawal ya yi wa marigayin addu'a Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Abin da Gwamna Dauda Lawal ya faɗa

A cikin wata sanarwar ta’aziyyar da gwamnan ya fitar, ya ce:

"Da zuciya mai cike da alhini na ke mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayi, Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da daukacin al’ummarmu bisa rasuwar Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji."

Gwamna Lawal ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin, ya kuma bai wa iyalan da ya bari juriyar jure rashin.

"Allah ya ji kansa, ya kuma bai wa iyalansa juriyar wannan babban rashi," in ji gwamnan.

Rasuwar Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji ta bar babban gibi a siyasar jihar Zamfara musamman mazabar Kauran Namoda ta Kudu da yake wakilta.

Tinubu ya yi alhinin rashin tsohon gwamna

A wani labarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar jihar Oyo bisa rasuwar tsohon gwamna, Dr. Victor Omololu Olunloyo.

Shugaba Tinubu ya bayyana Dr. Olunloyo a matsayin mutum mai hazaka, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ci gaban ilimi da kasa baki daya.

An ruwaito cewa marigayin ya ba da gudummuwa mai tarin yawa musamnan a fannin lissafi da kuma harkokin shugabanci da bunƙasa ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel