'Ba Mu Karyata Zulum ba,' Gwamnati Ta Yi Gyara kan Batun Dawowar Boko Haram

'Ba Mu Karyata Zulum ba,' Gwamnati Ta Yi Gyara kan Batun Dawowar Boko Haram

  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya musanta rahoton da ke danganta shi da sukar gwamna Babagana Zulum kan rashin tsaro
  • Gwamnan Borno ya bayyana fargabar cewa 'yan ta'addan Boko Haram su na kara karfi, tare da mamaye garuruwa da dama a jiharsa
  • A wani labarin daban, an ruwaito cewa Ministan ya caccaki kalaman gwamna Zulum, tare da cewa gwamnati na iya kokarinta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ofishin Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya yi martani kan rahoton da ke cewa Mohammed Idris, ya fatali da damuwar da Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum kan rashin tsaro.

A 'yan kwanakin nan ne gwamnan ya koka kan yadda mayakan Boko Haram ke kara karfi, kuma suna fatattakar jama'a daga garuruwansu, tare da zama a kauyukan.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi kakkausar martani ga Zulum kan hare haren Boko Haram

Borno
Gwamnatin tarayya ta musanta karyata gwamnan Borno kan rashin tsaro Hoto: The Governor of Borno State/Mohammed Idris fnipr
Asali: Facebook

A sakon da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X, Ofishin ya ce babu inda Ministan ya nemi a yi watsi da damuwar da Gwamna Babagana Zulum ke ciki kan rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin ya yi zargin cewa an fitar da rahoton cewa ya nemi a yi watsi da kalaman Zulum ne domin karkatar da hankalin al'umma daga aikin gwamnati wajen magance matsalolin tsaro.

Boko Haram: Gwamnati ta yi bayanin halin Borno

Arise News ta wallafa cewa a cikin amsarsa ga tambayoyin manema labarai game da kalaman Gwamna Zulum, Ministan Mohammed Idris ya ce gwamnati ta na bakin kokarinta.

Ya kara da cewa amma wannan ba ya nufin za a rasa matsalolin tsaro a wasu daga cikin sassan kasar nan daban daban.

Minista
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris Hoto: Mohammed Idris fnipr
Asali: Facebook

Ministan ya jadda cewa ana samun sauki ta hanyar kwazon aikin dakarun kasar nan.

Mohammed Idris ya kuma bayyana cewa gwamnati ta samar da kayan aikin tsaro, sannan ana kara samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Ya kuma tabbatar da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar kawar da ta'addanci da kuma samun nasara wajen yaki da fasa kwauri a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnati ta nemi hadin kan jama'a

Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a a kuma bukaci dukakannin masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatocin jihohi, su ci gaba da hada kai da gwamnatin tarayya.

Sanarawar da Ofishin Ministan ya fitar ta ce ta haka ne kawai za a tabbatar da zaman lafiya mai dore wa a tsakanin al'ummar kasar nan.

Ofishin Ministan ya yi kira ga kafafen yada labarai da su kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar guje wa kirkirar labaran da ba su da tushe, tare da yada bayanai na gaskiya.

Gwamnatin Borno ta koka kan rashin tsaro

A baya, kun samu labarin cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar hare-haren ƴan ta'addan Boko Haram da kara kafri da suke yi a jihar.

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi

A wani taron kwamitin tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Maiduguri, Gwamna Zulum ya nuna fargaba kan yadda ƴan Boko Haram ke kai wa hare-hare a manyan sansanonin sojoji.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata, inda ya yi kira kan cewa jihar tana cikin haɗarin komawa cikin rikici, ganin yadda hare-haren Boko Haram ke ƙara muni, wanda ya jefa su a cikin damuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng