Rundunar Sojoji Ta Yi Kakkausar Martani ga Zulum kan Hare Haren Boko Haram

Rundunar Sojoji Ta Yi Kakkausar Martani ga Zulum kan Hare Haren Boko Haram

  • Rundunar tsaro da Gwamna Babagana Umara Zulum sun yi sabani kan sake bayyanan hare-haren Boko Haram a jihar Borno
  • Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda 'yan ta'adda ke kai farmaki sansanonin sojoji, ana kashe mutane da sace-sace a yankuna
  • Sai dai a wani martani, rundunar ta ce jami’an tsaro na aiki tukuru wajen dawo da zaman lafiya a jihar da ma fadin kasar baki daya
  • Masana tsaro sun bayyana cewa dawo da 'yan Boko Haram cikin al’umma ba tare da hukunta su ba na kara jawo rashin zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Rundunar tsaro a Najeriya da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno sun yi sabani kan sake dawowar hare-haren Boko Haram a jihar.

Yayin da gwamnan ya ce jihar na fuskantar koma baya wajen yaki da 'yan ta'adda, rundunar ta ce gwamnati na kokari.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sanatan Borno ya taso ministan Tinubu a gaba kan sukar Gwamna Zulum

Rundunar tsaro ta martani ga Zulum game da Boko Haram
Rundunar tsaro ta bayyana kokarin sojoji kan yaki da Boko Haram. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Facebook

Zulum ya koka kan matsalar Boko Haram

Punch ta ce hakan ya biyo bayan nuna damuwa da Gwamna Zulum ya yi game da lalacewar tsaro a jiharsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake magana kan hare-haren, Gwamna Zulum ya bayyana cewa duk da taimakonsa ga sojoji, jihar tana fuskantar matsalar tsaro mai tsanani.

Yayin taron tsaro na musamman a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa ta taimaka matuka wajen yaki da Boko Haram cikin shekaru uku da suka wuce.

Zulum ya ce:

"Yayin da nake jawabi a nan, abin takaici ne ganin hare-haren Boko Haram da sace-sacen mutane sun zama kusan kullum ba tare da tsayawa ba."

Zulum ya koka kan hare-haren da suka faru a Wajirko, Sabon Gari, Wulgo da Izge, yana mai cewa kashe jama’a da jami’an tsaro na kara damunsa.

Ya ce:

"Kamar yadda kuka sani, gwamnatina ta kasance tana tallafawa sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da Boko Haram cikin shekaru uku da suka wuce."

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Rundunar tsaro ta bukaci yabawa jami'an sojoji kan yaki da Boko Haram
Rundunar tsaro bayyana kokarin sojoji game da yaki da Boko Harma. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum, HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Martanin rundunar tsaro kan hare-haren Boko Haram

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojoji na sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a Borno.

Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar Soji, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce dakarun suna aiki tukuru kuma ya kamata a yaba musu.

Ya ce ya kamata a yaba wa kokarin sojoji wajen yaki da ta’addanci da ake ci gaba da gudanarwa.

Ya ce:

"Sojoji suna sadaukar da ransu kan inganta tsaro wanda hakan ya kamata a yaba musu.
"Muna iya bakin kokarinmu, muna yin abin da ya kamata mu yi kuma muna ci gaba da yin hakan a kullum."

Sojoji sun gwabza da 'Yan Boko Haram

Kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan sojoji a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Miyagun sun kai harin ne kan sojojin rundunar 'Operation Hadin Kai' a ƙauyen Izge da ke cikin dajin Sambisa

An ce an hallaka aƙalla sojoji guda biyu, yayin da suka samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng