Jami'an Tsaro Sun Bude Wuta da Aka Yi Yunkurin Kai Hari Gidan Kashim Shettima
- Wani matashi ya yi tsaurin ido, har ya iya cire tsoro tare da yunkurin tsallaka wa gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima
- Rahotanni sun bayyana cewa matashin, mai suna Musa Ibrahim, ya kama katangar wani bangare na gidan Kashim a birnin Maiduguri
- Sai dai jami'an tsaro sun yi gaggawar hango shi, kuma nan take suka bude wuta a yunkurin hana shi tserewa tare da neman mafaka a gari
- Zuwa yanzu, an mika matashin, mai shekaru 35, zuwa asibiti, yayin da ake kokarin gano ko yana aiki ne tare da wasu bata-gari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'ian tsaro sun kai agajin gaggawa bayan da aka lura da wani matashi mai suna Musa Ibrahim, da ya yi kokarin kutsawa cikin gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Borno.
Lamarin ya faru ne da safiyar Talata, 9 ga Afrilu, misalin karfe 5:30 na safe, a gidan mataimakin shugaban kasa da ke New GRA, unguwar Gwange 3, kusa da titin Bama, a birnin Maiduguri.

Asali: Facebook
A cewar Zagazola Makama a shafinsa na X, matashin, mai shekaru 35 da haihuwa ya yi yunkurin haurawa katangar gidan ne ta gefen kogin Gadabul, da ke yammacin gidan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke mai shirin kutsawa gidan Kashim Shettima
Daily Post ta wallafa cewa motsin mutumin, wanda ya nuna alamun rashin gaskiya ne ya jawo hankalin jami'an tsaron da ake kai kawo a wajen.
Da ya hangi jami’an tsaron, Musa Ibrahim ya yi yunkurin guduwa, amma suka gaggauta daukar mataki.
Rahotannin sun ce domin hana shi tserewa, jami'an tsaro sun harbi matashin a kafarsa, suka kuma kama shi nan take domin gudanar da cikakken bincike.
Matashin da ya nemi haura gidan Kashim ya na asibiti
Bayan cafke shi, jami'an tsaro sun garzaya da da Musa Ibrahim zuwa Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri (UMTH), inda yake karbar magani a halin yanzu.
Har yanzu ba a san dalilin kutsawar sa cikin gidan ba, amma tuni aka mika lamarin ga Sashen binciken laifuffuka na jiha (SCID) domin gudanar da bincike mai zurfi.

Asali: Facebook
Hukumomi na kokarin gano ko Musa Ibrahim ya aikata yunkurin ne shi kadai ko kuma akwai wata babbar makarkashiya a kasa.
A martanin jami'an tsaro kan lamarin, an sake tsaurara tsaro a gidan mataimakin shugaban kasa domin hana aukuwar makamancin wannan a gaba.
Yadda Arewa za ta taimaki Kashim Shettima
A wani labarin kuma, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana Kashim Shettima a matsayin wakilin Arewa lamba ɗaya a matakin tarayya da ke bukatar goyon baya.
Yake cewa, a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana aiki wajen ci gaban Arewa da kuma tabbatar da ganin an samar da dama ga dukkanin al’ummomin yankin.
Shehu Sani ya yi kira ga al’ummar Arewa su kasance masu jajircewa wajen goyon bayan Kashim Shettima, domin tabbatar da ci gaban yankin da kuma Najeriya baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng