"Ya Ɗauka Ni ne," Abin da Ya Faru da Ɗiyar Buba Galadima Ta Kira Tinubu a Wayar Salula

"Ya Ɗauka Ni ne," Abin da Ya Faru da Ɗiyar Buba Galadima Ta Kira Tinubu a Wayar Salula

  • Jagora a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaka mai ƙarfi tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Ya ce shugaban kasar na girmama shi matuƙa, da hakan ya sa ya taimaka wajen sama wa ɗaya daga cikin 'ya'yansa aiki a bangaren kula da albarkatun mai
  • Buba ya kwatanta Tinubu da gwamnatin Muhammadu Buhari, tare da zargin cewa an hana daya daga cikin 'ya'yansa albashin aiki da Yemi Osinbajo

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaKusa da jam’iyyar NNPP kuma makusanci ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaka da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Buba Galadima ya ce duk da kasancewarsa a jam’iyyar adawa, babu wani abu da zai nema a wajen shugaban kasa ya rasa.

Kara karanta wannan

Mai magana da yawun PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tona asirin wasu shugabanni

Galadima
Buba Galadima ya ce har yanzu shi abokin Bola Tinubu ne Hoto: NNPP Kwankwasiyya/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da AIT, ya bayyana yadda Tinubu ya sama wa ɗaya daga cikin ’ya’yansa aiki bayan ta kira sh ta wayar salula.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yaran Buba Galadima suka tuntubi Tinubu

A bidiyon da Ayekooto ya wallafa a shafin X, Galadima ya ce ɗaya daga cikin yaransa ta nemi tallafi daga shugaban kasa Tinubu, kuma ya share mata hawaye.

Ya ce:

“Mu abokai ne, kuma za mu ci gaba da abota. Duk abin da na nema a wajensa, zan samu.”

Galadima ya ci gaba da bayani cewa:

“Akwai diyata da ta nemi aiki a bangaren man fetur, su biyu ne – ɗaya likita ce. Suka duba waya ta, suka ga lambar shugaban kasa. Sun kira shi suka ce su 'ya'yansa ne, saboda gari ya yi zafi.”

Tinubu ya sama wa diyar Buba Galadima aiki

Galadima ya ce ɗaya daga cikin yaransa da ta kammala NYSC ta shaida wa shugaban kasa cewa ta gaza samun aiki a hukumar da ke kula da harkokin man fetur, wacce Injiniya Gbenga Komolafe ke jagoranta.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Galadima
Jagora a NNPP, Alhaji Buba Galadima Hoto: NNPP Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Buba Galadima ya ce:

“Shugaban kasa ya ce a kira Komolafe, ya umarce shi ya ba diyata aiki. Wannan ya sa take so mu je Saudiyya ta gode wa Allah, ta gode wa Tinubu.”

A gefe guda, Galadima ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ’ya’yansa ta yi aiki a ofishin Yemi Osinbajo kusan kyauta.

Ya bayyana cewa gwamnati ba a taba biyanta albashin hakkinta ba har ta kammala aikinta a gwamnatin da ta gabata.

Tinubu ya gayyaci Buba Galadima kafin zabe

Galadima ya kuma bayyana cewa sau huɗu Bola Tinubu ya nemi ya shiga tafiyarsa tun kafin ya zama shugaban kasa.

Ya ce:

“Ban ga Tinubu a ido ba tun da ya zama shugaban kasa, amma a lokacin bikin binne mahaifiyar Nduka, sau huɗu yana barin inda yake ya zo inda nake yana roƙon mu yi tafiya tare, amma nace a’a.”

Buba Galadima: Shirin wasu a gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

A wani labarin, mun ruwaito cewa jigo a NNPP, Buba Galadima, ya zargi wasu da yunkurin haifar da rikici a jihar Kano domin ƙirƙirar dalilin da zai kai ga ayyana dokar ta-baci.

Buba Galadima ya bayyana cewa an gudanar da wani sirrin taro a birnin tarayya Abuja, wanda nufinsa shi ne tayar da zaune tsaye, wanda zai ba da damar mayar da Kano kamar Ribas.

Galadima ya kara da cewa a yayin taron da aka gudanar a Abuja, an yanke shawarar tura wanda ake shirin nada sarki zuwa Umrah domin ya nesanta kansa daga rikicin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng