Gwamnatin Tinubu Za Ta Ɗauki Sababbin Ma'aikata a Faɗin Najeriya, An Fitar da Sanarwa

Gwamnatin Tinubu Za Ta Ɗauki Sababbin Ma'aikata a Faɗin Najeriya, An Fitar da Sanarwa

  • Da alama kwanan nan Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki sabbabin ma'aikata a manyan makarantun Najeriya domin cike gurabe da giɓin da ake da su
  • Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya umarci makarantun da aka ba izinin ɗaukar ma’aikata su sanar da guraben aikin da suke nema ta hanyar talla ga jama'a
  • Rahoton da Legit Hausa ra tattara ya nuna cewa wannan umarni yana da nufin tabbatar da tsarin ɗaukar aiki mai gaskiya, bude kofa ga kowa, da adalci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa kan shirye-shiryen ɗaukar sababbin ma'aikata a wasu daga cikin manyan makarantun gaba da sakandire.

Ministan Ilimi na Najeriya, Tunji Alausa, ya umarci dukkan manyan makarantu Gwamnatin Tarayya da aka ba su izinin daukar ma’aikata su yi tallar guraben da suke nema.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Tunji Alausa.
Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki sababbin ma'aikata a manyan makarantun Najeriya Hoto: Tunji Alausa
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar yaɗa labarai ta wallafa a shafin X mai ɗauke da sa hannun daraktan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilimi, Boriowo Folasade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta fitar da tsarin ɗaukar aiki

Ministan ya buƙaci makarantun da suka sami izinin su bayyana dukkan guraben da suke nema ta hanyar tallatawa jama'a a kafafen sada zumunda shafukan yanar gizo.

Ya umurce su da su wallafa guraben a cikin jaridar ƙasa aƙalla guda ɗaya, shafukan intanet na makarantu da kuma a mujallu na ilimi da na ƙwararru masu alaƙa da aikin.

Wannan mataki yana da nufin tabbatar da gaskiya, buɗaɗɗen tsarin daukar aiki, da kuma bai wa dukkan ’yan Najeriya da suka cancanta damar neman aiki cikin adalci.

Tinubu ya ba makarantu izinin ɗaukar ma'aikata

Sanrwar ta bayyana cewa wannan umarni ya biyo bayan izinin da aka bayar ga manyan makarantun bisa ga bukatun da suka gabatar dangane da karancin ma’aikata da suke fama da shi.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur zai ƙara araha a Najeriya da Gwamnatin Tinubu ta dawo da tsarinta

Ta ce matakin yana cikin alkawarin da ma’aikatar ilimi ta dauka na inganta karfin cibiyoyin ilimi na ƙasa.

Sanarwar ta ce:

"Muna tunatar da dukkan manyan makarantu na gaba da sakandare mallakar Gwamnatin Tarayya su gabatar da bukatunsu na daukar ma’aikata ga ma’aikatar domin tantancewa.
"Ma’aikata ta shimfiɗa ingantattun hanyoyin tabbatar da bin doka, kuma ba za ta yi jinkiri wajen hukunta kowacce makaranta da ba za ta bi wannan umarnin ba.
"Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan al’amuran da suka shafi tsarin ilimi na manyan makarantu a Najeriya.

Tinubu ya samar da ayyukan yi miliyan 10

A wani labarin, kun.ji cewa fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa tsare-tsaren da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su za su samar da ayyukan yi miliyan 10.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya faɗi hakan da yake martani kan kalaman Kungiyar Bishof na darikar Katolika (CBCN).

Fadar Shugaban Kasa ta ce Najeriya ta samu ci gaba sosai tun bayan hawan Bola Ahmed Tinubu kan mulki a karshen watan Mayun 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng