"Akwai Talauci a Najeriya": Peter Obi Ya Fadi Yadda Rayuwa Ta Sauya Masa

"Akwai Talauci a Najeriya": Peter Obi Ya Fadi Yadda Rayuwa Ta Sauya Masa

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya taɓo batun talaucin da ake fama ɗa shi a Najeriya
  • Peter Obi ya bayyana cewa abubuwa sun taɓarɓare a ƙasar nan kuma mutane kullum ƙara talaucewa suke yi
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya kan su riƙa fitowa suna faɗin albarkacin bakinsu idan sun ga abubuwa ba su tafiya daidai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koka kan talaucin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Peter Obi ya bayyana cewa halin wahala da talaucin da ake fama da shi a Najeriya abin tayar da hankali ne.

Peter Obi ya koka kan tsadar rayuwa
Peter Obi ya ce talauci ya yi yawa a Najeriya Hoto: @peterobi
Asali: Facebook

An ga Peter Obi a taron LP - NEC

Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar LP wansa aka gudanar a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gama magana, ya faɗi matsayarsa kan ficewa daga LP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya kuma samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar LP wacce ke yin adawa a Najeriya.

Taron kwamitin na NEC ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Farfesa Nenadi Usman, tsohuwar ministar kuɗi kuma shugabar kwamitin riƙon kwarya na jam’iyyar.

Peter Obi ya ce akwai talauci a Najeriya

Da yake magana a wajen taron, Peter Obi ya koka kan irin yadda abubuwa suka taɓarɓare da kuma ƙara talaucewa da mutane ke yi, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

A cewarsa, abubuwa sun taɓarɓare sosai a ƙasar nan, don haka lokaci ya yi da za a haɗa kai domin a yi abinda ya dace.

“Dole mu riƙa magana idan abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata. Najeriya tana durƙushewa."
"Bayanan a bayyane suke, alƙaluma sun nuna komai, mutane na ƙara shiga cikin talauci kowace rana.”
“Wuraren da nake zuwa inda mutane ke tambayata, ‘Oga, za ka ci abinci? Za ka sha ruwa?’ yanzu ba wanda ke tambayata komai."

Kara karanta wannan

Babban basaraken Igbo ya gargadi 'yan Arewa kan kisan mafarauta a Edo? An ji gaskiya

"Wasu da suke kirana mu ci mu sha tare, yanzu idan suka gan ni, sai su nemi na ba su wani abu. Wannan yana nuna muku yadda rayuwa ta taɓarɓare."
"Don haka mu sani cewa abubuwa sun taɓarɓare. Al’amura suna cikin mawuyacin hali. Mu haɗa kai mu tabbatar cewa abubuwa na tafiya daidai, tun daga cikin jam’iyyarmu."

- Peter Obi

Peter Obi
Peter Obi ya koka kan talauci a Najeriya Hoto: @peterobi
Asali: Twitter

Peter Obi ya buƙaci a cire tsoro

Peter Obi ya kuma shawarci mambobin jam’iyyar da ka da su ji tsoron kowa, inda ya bayyana cewa:

“Ka da ku ji tsoron kowa. Waɗanda suka ji tsoro jiya ba su yi wani abin kirki ba. Dole mu riƙa magana idan abubuwa na tafiya ba daidai ba. Najeriya ta kamo hanyar durƙushewa."

LP: Peter Obi ya taɓo batun sauya-sheka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi wanda ya yi takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya yi magana kan jita-jitar cewa zai fice daga jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya dauko hanyar faranta ran ma'aikatan da suka yi ritaya a Kaduna

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai raba gari da LP.

Ya bayyana cewa bai taɓa yin magana da wani ko wata ƙungiya ba kan cewa zai bar LP zuwa wata jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng