'Mun Yi Kuskure,' Gwamnatin Tinubu Ta ba da Hakuri kan Maganar Nada Mukamai
- Fadar shugaban kasa ta ce Bola Tinubu ba ya nuna wariyar addini ko kabila wajen nada mukamai tun da ya hau karagar mulki
- Gwamnatin tarayya ta ce tun yana Gwamnan Legas, ya bai wa kowa dama, tare da bai wa ’yan kowane yanki mukamai bisa cancanta
- A kokarin fitar da adadin mutanen da Bola Tinubu ya nada a Arewa da Kudu, gwamnatin ta yi kuskure kuma ta ba 'yan Najeriya hakuri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Bola Tinubu na tafiya ne bisa tsarin adalci da daidaito, musamman a bangaren nadin mukamai.
Ta ce la’akari da tarihin Tinubu tun yana Gwamnan Jihar Legas, ba a taɓa ganin nuna wariya daga gare shi ba, domin ya rika bai wa mutane mukamai ba tare da la’akari da kabilarsu ba.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da hadimin Bola Tinubu, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunday Dare ya ce irin akidar da Bola Tinubu ya kafa a Legas wajen raba mukami ta ci gaba da bayyana a salon nadin manyan mukamai tun bayan hawansa karagar mulki a 2023.
'Tinubu bai nuna wariya,' Sunday Dare
Fadar shugaban kasa ta ce shugabancin da Tinubu ke yi ya bayyana cewa bai nuna bambancin addini ko kabila ba, domin yana ganin Najeriya a matsayin kasa da ke bukatar hadin kai.
Sanarwar da ta fitar ta nuna cewa:
“Duk da cewa mutane suna kallon nadin da aka yi zuwa yanzu da kallo na kabilanci ko yanki, ya kamata a fahimci cewa wa’adin Tinubu bai cika shekaru biyu ba,
"Kuma akwai karin mukamai da za nada a gaba.”
Sanarwar ta kara da cewa shugaban kasa ya fahimci nasararsa ta fito ne daga dukkan sassan Najeriya, don haka yana kokarin hada kan kasa ta hanyar rarraba mukamai bisa cancanta.

Asali: Facebook
Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri
Yayin kokarin bayyana mutanen da Bola Tinubu ya ba mukamai, hadimin shugaban kasa ya yi kuskure wajen fadin adadin.
A karkashin haka, Sunday Dare ya wallafa a X cewa a nan gaba kadan za su gyara kuskuren domin fitar da sahihin adadin wadanda aka nada.
Adadin da Dare ya wallafa a farko
A karon farko, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Arewacin Najeriya ya fi samun kaso mafi yawa cikin mukaman da aka raba.
A cewar hadimin shugaban kasa, daga cikin mukamai 134 da aka nada zuwa yanzu, Arewa ta samu guda 71, yayin da Kudu ta samu 63.
Ndume ya zargi Tinubu da nuna wariya
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da nuna bambanci wajen nada mukaman gwamnati.
Ali Ndume ya ce ba wai kawai zargi yake yi wa Bola Tinubu, ya ce ya nuna alkaluma da suka tabbatar da cewa ana fifita wasu yankuna wajen nada mukamai.
Sanatan ya bayyana cewa ya san za a samu masu sukarsa bayan ya yi bayanin, amma ya ce hakkinsa ne ya fito ya fada wa gwamnati gaskiya saboda a kan haka aka zabe shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng