Gwamnatin Tinubu za Ta Kawo Tallafin N300bn, Mutum 1 zai iya Samun N10m
- Gwamnatin Tarayya na shirin kaddamar da asusun N300bn domin tallafa wa matasan da suka kammala jami’a, su kafa kasuwanci
- Duk wanda aka tabbatar ya cancanta zai iya samun N10m ko ma fiye da haka domin sauƙaƙa masa kafa sana’a da zai dogara da kansa
- Ministan Ilimi na kasa, Dr Tunji Alausa, ya ce wannan yunkuri wani bangare ne na shirin Bola Tinubu na sauya fasalin tattalin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin kafa wani asusun biliyoyin Naira domin taimaka wa matasa da suka kammala karatu su zama masu dogaro da kai.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da laccar yaye dalibai karo na 28 a Jami’ar Jihar Legas (LASU) da ke Ojo.

Asali: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa ciki har da shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tunji Alausa ya ce asusun da aka tanada zai taimaka wajen karfafa matasa su kafa sana’o’i masu zaman kansu.
Mutum zai iya samun tallafin N10m
Dr. Alausa ya ce za a bude asusun ne da zunzurutun kudi har N300bn, inda kowanne mutum da ya cancanta zai iya samun tallafin N10m ko ma fiye da haka domin kafa kasuwanci.
Ministan ya ce:
“Asusun wani bangare ne na gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi domin janyo hankalin matasa da samar musu da hanyoyin dogaro da kai.”
Ya kara da cewa, matakin zai taimaka wajen rage radadin rashin ayyukan yi da ke addabar matasa da kuma bunkasa tattalin arziki ta hanyar sana’o’i da kere-kere.
'Ilimi muhimmin abu ne wajen gina kasa,' Minista
A cikin laccar da ya yi, Dr. Alausa ya bayyana ilimi a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen samar da ɗa mai kishin ƙasa.
Ya ce:
“Kishin ƙasa ba wai rike tutar ƙasa da rawa ba ne kawai, a’a, yin abubuwan da ke amfanar ƙasa ne.
Haka kuma, ɗan ƙasa mai kishi yana bin doka, yana da biyayya da kuma kare dukiyar ƙasa.”
Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bai wa bangaren ilimi muhimmanci, tare da tabbatar da inganci da kuma ƙarfafa horar da matasa a fannoni na fasaha da koyon sana’a.
An raba sama da N45bn a shirin NELFUND
Dr. Alausa ya ce halin yanzu, an raba fiye da N45bn a cikin shirin bayar da lamuni ga ɗalibai na NELFUND.
Ya ce hakan wani ƙarin mataki ne da ke tabbatar da cewa gwamnati na jajircewa wajen ganin ba a bar kowa a baya ba a harkar ilimi.
A nata jawabin, Shugabar Jami’ar LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello, ta ce ya kamata 'yan Najeriya su nuna kishin kasa.
Shi ma shugaban taron, Dr Abdullahi Ganduje, wanda kuma shi ne Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce ilimi ne mafita ga matsalolin ɗan adam.

Asali: Twitter
Ndume ya zargi Tinubu da nuna wariya
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Muhammad Ndume ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan nada mukamai.
Ali Ndume ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita wasu yankuna da mukamai a kan wasu bangarori na Najeriya.
Baya ga haka, Ndume ya ce ya fadi maganar ne a matsayinsa na mai kishin kasa kuma ba ya jin tsoron abin da zai biyo baya.
Asali: Legit.ng