Galadiman Kano: Sarakuna, Yan Siyasa da Suka Je Fadar Aminu Ado maimakon Sanusi II

Galadiman Kano: Sarakuna, Yan Siyasa da Suka Je Fadar Aminu Ado maimakon Sanusi II

  • Mutuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi ta jefa al’ummar jihar cikin jimami da alhini duba da girman dattijon a gare su
  • Sarakunan gargajiya da wasu ’yan siyasa sun rarrabu wurin yin jaje ga Sarakunan Kano biyu da ke rigimar sarauta da juna
  • A bangarensa, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya dakatar da shagulgulan sallah domin karbar ta’aziyyar Galadima

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An sanar da rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Galadima a ranar Talata 1 ga watan Afrilun shekarar 2025.

Tun bayan sanar da rasuwar, al'ummar Kano suka ci gaba da jimami kan babban rashin da aka yi na dattjon.

Al'umma da dama sun yi jimamin rasuwar Galadiman Kano
Bayan rasuwar Galadiman Kano, yan siyasa da sarakuna sun kai ziyarar jaje. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

'Yan siyasa, sarakuna sun yi jimamin Galadiman Kano

Yan siyasa da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana alhininsu kan rashin daya daga cikin manyan masu sarauta a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an dan samu rarrabuwar kawuna yayin da wasu suka ziyarci fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero domin yi masa jaje.

Wasu kuwa daga cikin sarakunan gargajiya da yan siyasa sun zabi zuwa fadar Sarki Muhammadu Sanusi II domin jajanta masa.

Galadiman Kano: Aminu Ado ya soke bikin sallah

Har ila yau, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya dakatar da bukukuwan da ya shirya yi a fadar Nasarawa domin ci gaba karbar ta'aziyya.

Hakan ya ba basaraken damar karbar al'umma ciki har da 'yan siyasa da suke ta tururwa zuwa fadarsa.

Legit Hausa ta jero muku wadanda suka kauracewa fadar Sanusi II domin jaje a fadar Aminu Ado yayin da wasu suka hada duka.

1. Abdullahi Umar Ganduje

Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya dura a Kano a ranar Asabar 5 ga watan Afrilun 2025.

Ganduje ya wuce kai tsaye fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero bayan ya sauka daga filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

'Masarauta ta girmi haka': Shehu Sani kan gayyatar Sarki Sanusi II, ya nemo mafita

Ganduje ya samu rakiyar jiga-jigan jam'iyyar APC domin jajantawa gwamnatin Kano da masarauta da sauran al'umma kan rashin da aka yi.

Ganduje ya ziyarci fadar Aminu Ado a Kano
Abdullahi Ganduje ya kai ziyara fadar Aminu Ado domin jaje kan rasuwar Galadiman Kano. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

2. Hon. Alhassan Ado Doguwa

Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Alhassan Ado Doguwa shi ma ya ziyarci fadar domin yin jaje kan rashin da aka yi.

Ado Doguwa ya jajantawa Aminu Ado Bayero kan rashin da aka yi inda ya ce tabbas an rasa dattijo a Kano.

3. Alhaji Tanko Yakasai

Dattijo a jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya samu damar kai ziyara fadar Aminu Ado Bayero kan rashin Galadiman Kano.

Dattijon ya jajantawa basaraken kan rashin da aka yi a fadarsa a ranar 3 ga watan Afrilun 2025.

Dattijo Tanko Yakasai ya ziyarci fadar Aminu Ado
Alhaji Tanko Yakasai ya jajantawa Aminu Ao kan rasuwar Galadiman Kano. Hoto: @HrhBayero.
Asali: Twitter

4. Sanata Kawu Sumaila

Daga cikin yan siyasa da suka ziyarci fadar Aminu Ado akwai Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kawu Sumaila domin mika nasa sakon jaje.

Sai dai Kawu Sumaila ya kuma kai ziyarar jaje fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a ranar 4 ga watan Afrilun 2025 domin yi masa jaje kan rashin da aka yi.

Kara karanta wannan

Galadiman Kano: Bayan korafi, Ganduje ya dura a Kano, ya wuce fadar Aminu Ado

5. Sarkin Hadejia

Mai Martaba Sarkin Hadejia ya jajantawa Aminu Ado Bayero a fadarsa kan rashin Galadiman Kano da aka yi.

Basaraken ya tura tawaga ne ta musamman ne da wakilcin inda suka yi addu'ar ubangiji ya jikan Galadiman Kano.

Har ila yau, tawagar Sarkin Hadejia ta kai ziyarar jaje ga Sanusi II domin yi masa ta'aziyya kan rashin Galadiman Kano.

Rahoton Legit Hausa ya ce wakilan Sarkin Hadejia, Dr. Alhaji Adamu Abubakar Maje sun isa fadar basaraken domin yi masa ta'aziyya kan babban rashin da aka yi.

Sanarwar da shafin Masarautar Kano ya wallafa a X, ta ce:

"Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayaro CFR CNOL JP ya na ci gaba da karbar ta’aziya, Mai Martaba Sarki ya karbi wakilan Mai Martaba Sarkin Hadejia Dr. Alh. Adamu Abubakar Maje CON bisa Wakilcin Galadiman Hadejia."

Sanusi II ya nada sabon Galadiman Kano

Kara karanta wannan

Galadima: Aminu Ado na karbar ta'aziyya a fadarsa, sarakuna, 'yan siyasa na tururuwa

Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi sababbin nade-nade a masarauta, ciki har da ɗansa Adam Lamido Sanusi (Ashraf).

A cikin wata Sanarwa da masarautar ta fitar ta bayyana cewa an nada Ashraf Sanusi a matsayin sabon Tafidan Kano.

Nade-naden sun hada da Munir Sanusi Bayero da aka sauya daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano, Kabiru Tijjani Hashim daga Turakin Kano zuwa Wambai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng