Rundunar 'Yan Sanda Ta Yi Babban Kamu a Kano, An Bankado Masu Safarar Makamai
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gano wata ƙungiya da ke safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Dorayi Babba, jihar Kano
- Jami’an tsaro sun cafke Abdul Sadiq, Ahmad Muazu, da Aliyu Sharif, an ƙwato makamai da harsasai da ake zargin an aikata laifi da wasunsu
- Kakakin rundunar 'yan sandan kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce sahihan bayanai daga jama’a ne suka taimaka wajen nasarar samamen
- Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya ce rundunar za ta ci gaba da kai samame don hana yaduwar makamai ba bisa ƙa’ida ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta gano wata ƙungiyar masu safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke da mafaka a jihar Kano.
Wannan bincike ya kai ga cafke mutane uku da ake zargi tare da ƙwato bindigu 15 da aka ƙera a gida da kuma harsasai 102.

Asali: Facebook
A cewar wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook, wadanda aka kama sun hada da Abdul Sadiq mai shekaru 43, Ahmad Muazu mai shekaru 22, da Aliyu Sharif mai shekaru 40.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke masu safarar makamai a Kano
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kama waɗannan mutanen ne a ranar 10 ga Afrilu a unguwar Dorayi Babba a karamar hukumar Gwale da ke jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da cewa an gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri da suka kai ga gano makaman.
Ya ce:
“An kama waɗanda ake zargi da tarin makamai da ba su da lasisi."
“Masu bincike na ci gaba da kokarin gano inda ake kera makaman da kuma kama sauran masu hannu a lamarin.”

Kara karanta wannan
Yan sanda sun yi ƙarin haske bayan kama wasu mafarauta 4 daga Kano da makamai a Edo
Sauran makaman da aka kama a Kano
Baya ga makaman da aka ƙwato, an kuma samu harsasai shida da aka harba a baya, waɗanda ake kyautata zaton an yi amfani da su wajen aikata laifuka.
Sufeto-Janar na ‘yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya yaba da gaggawar da jami’an suka nuna wajen gudanar da aikin da cafke wadanda ake zargi.

Asali: Facebook
Ya sake jaddada kudirin rundunar na dakile yaduwar makamai ba bisa ƙa’ida ba a fadin kasar domin kare rayukan jama'a.
Sufeto-Janar na ‘yan sandan ya tabbatar wa da al’umma cewa ‘yan sanda za su ci gaba da kai samame a kan ƙungiyoyin masu aikata laifi tare da dawo da zaman lafiya a sassan ƙasar nan.
Gwamnatin Kano ta yi martani ga ECOWAS
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta bayyana matsayinta kan hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke game da dokar batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da jihar ta kafa.

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya ce jihar ba za ta amince da wani nau’i na matsin lamba daga kowace kungiya ko ƙasa ba dangane da wannan doka.
Kotun ECOWAS dai ta yanke hukunci cewa wasu sassa na dokar batanci da sauran dokokin laifuffuka a ƙarƙashin tsarin Shari’a na jihar Kano sun saba da ka’idojin kare hakkin ɗan Adam.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng