An Fara Mantawa: Lauya Ya Taso da Maganar Kisan Hausawa a Edo da Tambayoyi 10

An Fara Mantawa: Lauya Ya Taso da Maganar Kisan Hausawa a Edo da Tambayoyi 10

  • Abba Hikima ya bukaci bayani kan yadda ake shirin gurfanar da wadanda ake zargi da kisan Hausawa a Uromi, jihar Edo
  • Jama’a sun caccaki rashin magana daga wajen sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, da kuma hukumomin tsaro
  • Wasu sun ce ana yawan mantawa da kashe-kashen da suka shafi Arewacin Najeriya, musamman idan ‘yan yankin aka kashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da al’umma ke fara mantawa da harin da aka kai wa wasu Hausawa a Uromi, jihar Edo, an fara dawowa da batun.

Lauya mai kare hakkin dan Adam, Abba Hikima, ya fito fili da tambayoyi 10 masu nauyi domin zaburar da jama'a da hukumomi.

Abba Hikima
Abba Hikima ya yi tambayoyi kan Hausawan da aka kashe a Edo. Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa Abba Hikima ya yi tambayoyin ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane na ci gaba da nuna damuwa kan yadda 'yan Arewa suka dauki lamarin duk da muhimmancinsa.

Haka zalika wasu sun yi magana kan rashin samun cikakken bayani kan matakan da ake dauka domin hukunta wadanda suka aikata kisan a baya bayan nan.

Abba Hikima da ya shahara wajen kare hakkin jama’a, ya bayyana cewa irin wannan shiru yana rage karfin bincike da adalci a Najeriya.

Kisan Uromi: Tambayoyi 10 daga Abba Hikima

A rubutun da ya yi, Abba Hikima ya ce an shafe kwanaki 12 da kisan Hausawa a Uromi, sai ya lissafo tambayoyi kamar haka:

1. Ina wadanda aka kama?

2. Su nawa ne?

3. Me ake shirin yi da su?

4. Ina rahoton ‘yan sanda?

5. Ina kwamitin Kano?

6. Ina sunayen mamatan?

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

7. Su nawa ne?

8. A wane hali iyalinsu suke?

9. Ina aka kwana?

10. Ina? Ina? Ina?

Lauyan ya ce irin wannan shiru ne ke jawo bincike ya shiririce a Najeriya.

Martanin jama'a kan tambayoyin Abba Hikima

Bayan rubutun, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu inda Mahmud Zukogi ya ce:

“Har yanzu ba mu ji ko kalma daga bakin Sanata Oshiomhole ba, wanda ke wakiltar Edo ta Arewa. Ma fi muni, ba mu san ko ya shiga tawagar gwamna zuwa Kano ba.”

Hassan Abubakar Karaye ya ce:

“Ku masu alkalami da murya, ku bibiyi wannan lamari. Allah ya jikansu.”

Wasu sun koka kan yadda kisan Hausawa ko ‘yan Arewa ke wucewa ba tare da daukar mataki ba a Najeriya.

Zakariyya Sani ya ce:

“A jiya Fulani ‘yan bindiga sun kashe mutane a Katsina, shiru kake ji – ko kafafen sadarwa labarin bai girgiza ba.”

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

Yusuf Yahaya Alarammah ya kara da cewa:

“A washe garin kisan Edo, an kuma kashe Musulmi ‘yan Arewa a Abuja yayin zanga-zanga lumana. Ya kamata a dinga tabo duk wadannan abubuwa.”

Kisan Uromi: Sanata Barau ya raba miliyoyi

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin ya raba tallafi ga wadanda aka kashe wa iyalai a Edo.

Sanata Barau Jibrin ya ce ya raba Naira miliyan 1 ga iyalan kowane mamaci kai tsaye domin su rage radadin rayuwa.

Baya ga haka, ya bayyana cewa zai cigaba da bibiyar lamarin domin tabbatar da an yi adalci wajen hukunta wadanda suka aikata laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng