Kano: Buba Galadima Ya Yi Maganar Yiwuwar Sake Sauke Sanusi II da Maido Shi

Kano: Buba Galadima Ya Yi Maganar Yiwuwar Sake Sauke Sanusi II da Maido Shi

  • Buba Galadima ya ce akwai shirin cire Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano, amma idan da za a cire shi sau 10, za su dawo da shi
  • Ya bayyana cewa kotun da ke sauraron rikicin masarautar Kano na samun umarni daga Abuja ba tare da masaniyar shugaban ƙasa ba
  • Galadima ya musanta jita-jitar sabani tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa ana son dagula Kano ne kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana goyon bayansa ga mai martaba Muhammadu Sanusi II, yana mai cewa duk yunkuri na cire shi daga gadon sarauta zai ci tura.

Ya ce yunkurin hana Kano amfana da ribar dimokuradiyya ta hanyar rikicin sarauta ba zai yi nasara ba, domin NNPP na da cikakken tsari da karfi a jihar.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: An so rufe Sanusi II a Abuja, a saka dokar ta baci a Kano

Buba Galadima
Buba Galadima ya ce ko an sauke Sanusi II za su mayar da shi. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

Galadima ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da tashar AIT, ya ce jam’iyyarsu za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da adalci, duk da yunkurin rushe tsarin siyasa a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Za mu cigaba da maida Sanusi II,' Buba Galadima

Buba Galadima ya bayyana cewa wasu mutane na kokarin amfani da husumar da suke da ita da Muhammadu Sanusi II domin haifar da rikici a Kano.

A cewar Buba Galadima:

“Idan sun cire Sanusi II sau 10, za mu dawo da shi karo na 11. Ba za su iya yi masa komai ba.”

Ya kara da cewa akwai shaidu da ke nuna cewa umarnin da ake bai wa kotunan da ke sauraron rikicin masarautar Kano na zuwa ne daga Abuja, amma ba tare da sanin shugaba Bola Tinubu ba.

Akwai sabani tsakanin Abba da Kwankwaso?

Kara karanta wannan

An fara gargadin gwamnatin Tinubu kan hana shigo da kayan sola Najeriya

A yayin da ake yada jita-jitar cewa akwai sabani tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya musanta hakan.

Ya ce ba wani rikici ko baraka tsakaninsu, sai dai kawai akwai wasu mutane da ke da manufa ta siyasa na kokarin dagula jihar Kano.

Buba Galadima
Buba Galadima ya ce ba yau aka saba rikici a siyasar Kano ba. Hoto: Kwankwasiyya Reporters.
Asali: Facebook

Harkokin siyasar Kano a jiya da yau

Buba Galadima ya ce siyasar Kano ta daɗe tana fuskantar hayaniya da jayayya tun lokacin samun ‘yancin kai a Najeriya.

Ya tuna cewa har ma a zamanin Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, irin wannan rikici ya saba faruwa, yana nuni da cewa ba sabon abu ba ne.

Buba Galadima ya ce an so rufe Sanusi II a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce akwai masu neman hargitsa Kano domin a ayyana dokar ta baci a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

Buba Galadima ya yi zargin cewa 'yan sanda sun gayyaci Muhammadu Sanusi II zuwa Abuja ne domin a rufe shi.

A cewarsa, hakan na cikin matakin da wasu jami'an gwamnati suka dauka domin ganin Kano ta rikice ta yadda za a samu damar saka dokar ta-baci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng