Shugaba Tinubu Ya Kara Girmama Sheikh Idris Dutsen Tanshi, Ya Tura Nuhu Ribaɗu Gidansa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinibu ya tura Nuhu Ribadu zuwa gidan Marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi domin yi wa iyalansa ta'aziyya
- Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa Sheikh Idris Abokinsa ne na kusa amma ba kowa ya san haka ba, yana mai cewa an yi babban rashi
- Ziyarar dai ta ƙara nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke girmama marigayin saboda gudummawarsa wajen yaƙi da tsattsauran ra'ayi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya je ta'aziyya gidan marigayi Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a Bauchi.
Malam Ribadu ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya turo shi ya wakilce shi saboda yadda yake girmama malamin.

Asali: Facebook
Nuhu Ribaɗu ya bayyana marigayi Imam Idris Abdul’aziz Dutsen-Tanshi a matsayin abokinsa na kusa wanda za a yi matuƙar rashinsa, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman Nuhu Ribadu a gidan Dutsen Tanshi
Ya ce za a yi rashin Malamin saboda gaskiya da jajircewarsa wajen faɗin gaskiya, da kuma yadda ya tsaya tsayin daka wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayin addini.
Ribadu ya ce ba kowa ya san dangantakarsa da Malam Idris ba, don haka kaɗan ne daga cikin jama’a suka san cewa suna da kusanci, duk da cewa sun dade tare a matsayin abokai.
Yayin ziyarar ta’aziyya a gidan marigayin, Ribadu ya jajanta wa iyalan Shehin Malamin, ɗalibansa da kuma al’ummar Jihar Bauchi bisa rashin da suka yi.
Sheikh Idris Abdul’aziz ya rasu kimanin kwanaki biyar da suka gabata bayan fama da doguwar jinya.
Nuhu Ribadu ya wakilci Shugaba Tinubu
Ribadu ya bayyana Imam Idris Abdul’aziz a matsayin fitaccen malamin addini wanda karatunsa da hudubarsa suka karade yankunan da ake jin Hausa a Afirka ta Yamma da tsakiya.
“Abokina ne. Malami ne da ake girmamawa. Wa’azinsa ya kai ga kowane yanki da ake jin Hausa a Afirka.
"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya aiko ni in wakilce shi domin yana ƙasar waje," in ji Ribaɗu.

Asali: UGC
Gwamnatin Tarayya tana girmama Dutsen Tanshi
Ziyarar Ribadu ta nuna yadda Gwamnatin Tarayya ke daraja gudummawar da marigayin ya bayar wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi, ilimantarwa, da jagoranci na addini a sassa daban-daban na Afirka.
Haka nan, Dr IdrisAbdul’aziz ya shahara da hudubarsa masu zafi, da tsayin daka a kan gaskiya, da tasirinsa a fannin ilimin addinin Musulunci, musamman a Arewacin Najeriya.
A madadin iyalan marigayin, Malam Yau Idris ya yi godiya ƙwarai ga Shugaba Bola Tinubu bisa nuna damuwa da tausayawa da ya yi musu a wannan lokaci na alhini.
Gwamnoni 19 sun yi jimamin rasuwar Dutsen Tanshi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnoni 19 na jihohin Arewacin Najeriya sun yi ta'aziyyar rasuwar Dr. Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi.
Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce wannan rashi ne ya shafi dukkan ƴan Najeriya musamman musulmi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdaus.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng