Gwamnan Filato Ya Fayyace Komai, An Ji Yawan Garuruwan da 'Yan Ta'adda Suka Mamaye
- Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye garuruwa 64 a cikin jiharsa, kuma suna cin karensu babu babbaka
- A ranar 4 ga Afrilu, kungiyar ci gaban Bokkos (BCDC) ta bayar da rahoto ‘yan ta’adda sun kashe fiye da mutane 10, wanda adadinsu ya karu a yanzu
- Gwamnan Mutfwang ya bayyana damuwarsa game da hare-haren ta’addanci, ya bayyana cewa miyagun suna ci gaba da da ayyukansu hankali kwance
- Ya bayyana bukatar a samar da hadin kai yayin da ya roki jami'an tsaro da su tabbata a kawo karshen kisan kare dangin da ake yi wa mutanensa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Filato – Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye garuruwa 64 a cikin jiharsa.
Ya kara da cewa, kashe-kashen da aka yi a karamar hukuma ta Bokkos na kwanan nan, abu ne da wasu suka dauki nauyinsa a kokarin kisan kare dangi.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ya ruwaito cewa, kungiyar ci gaban Bokkos (BCDC) ta bayar da rahoton ranar 4 ga Afrilu cewa, ‘yan ta’adda sun kashe fiye da mutane 10, inda adadin wadanda suka mutu daga baya ya karu zuwa 52.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Filato ya fusata da ta'addanci a jiharsa
Channels Television ta ruwaito cewa, Gwamna Mutfwang ya zargi wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aikata wannan ta’addanci, wanda har yanzu ba a kai ga gano su ba.
Ya ce:
“Tambayar ita ce, waɗanne ne mutanen da ke bayan masu shirya wannan ta’addanci? Wannan shi ne abin da hukumomin tsaro za su taimaka mana wajen gano wa.”
'Yan ta’adda sun mamaye garuruwan Filato
Gwamnan jihar Filato ya bayyana cewa ‘yan ta’adda sun mamaye garuruwa 64 a cikin karamar hukumar Bokkos, Barkin Ladi, da Riyom, inda suka tilasta wa ‘yan kauyuka barin gidajensu.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Yanzu haka, akwai al’ummomi fiye da 64 da ‘yan ta’adda suka mamaye garuruwansu a cikin jihar Filato tsakanin karamar hukuma ta Bokkos, Barkin Ladi da Riyom.”
“Sun mamaye garuruwam, sun sake masu suna, kuma mutanen ('yan ta'adda) suna rayuwa cikin jin dadi a kan filaye da suka tilasta wa mutane barin su.”
Hare-haren baya-bayan nan a Filato ya ja hankalin kasar nan, ganin yadda aka jera kwanaki ana hallaka bayin Allah a kananan hukumomin jihar da dama.
Gwamna Muftwang ya bayyana cewa akwai bukatar samar da hadin kai da jami'an tsaro wajen kakkabe mugun aikin da ke ci gaba da tsorata mutane.
"Ana daukar nauyin ta'addanci," Gwamnan Filato
A baya, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya yi karin haske kan hare-haren ta’addanci da ake kai wa al’ummomi a cikin jiharsa, inda sama da mutum 60 suka rasu.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ana kai hare-haren kan bayin Allah a jiharsa ne a wani lamari mai kama da kisan kare dangi, lamarin da ke rusa zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce akwai ƙungiyoyi da wasu mutane da ke ɗaukar nauyin wannan ta’addanci, amma bai bayyana sunayensu ba zuwa yanzu, sai dai jami'an tsaro suna ci gaba da aikin zakulo su.
Asali: Legit.ng