'Yan Bindiga Sun Kai Hare Haren Ramuwar Gayya a Zamfara, Sun Yi Barna
- Ƴan bindiga na ci gaba da jin takaicin kisan da jami'an tsaro suka yi wa wasu daga cikin manyan jagororinsu a jihar Zamfara
- Tsagerun sun ƙaddamar da hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Tsafe domin yin ramuwar gayya
- Hare-haren na ƴan bindiga sun jawo asarar rayuka yayin da aka sace mutane sama da 60 zuwa cikin daji cikin 'yan kwanaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun ƙaddamar da jerin hare-hare a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da sama da mutum 60, a hare-haren ta'addancin da suka kai.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne domin ramuwar gayya kan kashe wasu daga cikin shugabanninsu da jami’an tsaro suka yi a baya-bayan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun samu nasarori kan ƴan bindiga
Daga cikin tantiran ƴan bindigan da aka kashe har da Kachalla Yellow (wanda aka fi sani da Dan Isuhu), wanda aka kashe kusan makonni biyu da suka wuce yayin wani yunƙurin kai harin kwanton ɓauna kan jami’an rundunar Askarawan Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shi tare da ɗan uwan sa, wanda shi ne ɗa a wajen Ado Aliero.
Wani babban ɗan bindiga da ba a ambaci sunansa ba, na daga cikin waɗanda jami'an tsaro suka kashe.
Ƴan bindiga sun kai hare-haren ɗaukar fansa
Tun bayan faruwar hakan, hare-haren ƴan bindiga da ake kyautata zaton mabiya shahararren ɗan bindigan nan Ado Aliero ne, sun ƙaru a faɗin ƙaramar hukumar Tsafe.
Harin baya-bayan nan ya auku ne a ranar Lahadi a ƙauyen Gidan Arne, inda ƴan bindiga suka harbe mutane uku.
Mutane biyu sun mutu nan take, yayin da na uku ke karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an sace mata kusan 40 a lokacin harin, kuma an ƙona gidaje da dama.

Asali: Facebook
A ranar da lamarin ya faru, wani hari na daban ya auku a ƙauyen Keta, mutum guda ya rasa ransa, an ƙona motoci 11, kuma ƴan bindigan sun fasa shaguna da dama suka sace kayayyaki.
Wani shugaban al’umma a Tsafe, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar da aukuwar hare-haren, kuma ya bayyana cewa an kai wasu irinsu a hare-haren a ƙauyukan Yan Doton Daji da Unguwan Chida.
Ya ce mutane 21 ne aka sace, inda aka sace mutum 11 a Yan Doton Daji, da kuma mutum 10 a Unguwan Chida, da ke kusa da garin Kucheri.
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun hallaka mutane 11 a harin da suka kai a ƙauyen Rijiya da ke cikin ƙaramar hukumar.
Miyagun ba su tsaya iya haka nan ba sai da suka ƙona makarantar firamare inda yara ke zuwa neman ilmi a ƙauyen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng