Kotu: Saura Kiris Shugabannin Kananan Hukumomin Kano Su San Makomarsu

Kotu: Saura Kiris Shugabannin Kananan Hukumomin Kano Su San Makomarsu

  • Kotun daukaka kara a Abuja ya dakatar da yanke hukunci kan korafe-korafe guda biyar da suka shafi zaben kananan hukumomi a Kano
  • Majalisar dokoki da babban lauyan Kano sun ce kotun tarayya ba ta da hurumin dakatar da KANSIEC daga gudanar da zabe
  • A hukuncin da kotun tarayyar ta yanke tun da farko, ta dakatar da KANSIEC daga gudanar da zaben saboda dalilan saba doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Kwamitin musamman na kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ya dakatar da yanke hukunci kan korafe-korafe guda biyar daga rikicin shari’a kan zaben kananan hukumomin Kano.

Korafe-korafen sun samo asali ne daga hukuncin kotun tarayya da ke Kano, inda a ciki aka soke nadin 'yan hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC).

Kara karanta wannan

Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers

Zaben
Kotu za ta yi hukunci kan zaben kananan hukumomin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa cikin shari’un da ke gaban kotun akwai karar lamba CA/KN/20/2025 da KANSIEC da wasu mutum biyar suka shigar a gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata karar kuma mai lamba CA/KN/233/2024, Majalisar Dokokin Jihar Kano da wani bangare suka shigar, inda Aminu Aliyu Tiga da wasu mutane 14 ke matsayin wadanda ake kara.

An shigar da kara kan zaben Kano

The Nation ta wallafa cewa haka kuma akwai kara mai lamba CA/KN/290/2024 wacce babban lauya na Kano da wasu mutane shida suka shigar kan jam’iyyar APC da wasu mutum uku.

Haka zalika, an shigar da kara lamba CA/KN/291/2024 daga KANSIEC da wasu mutum takwas, Majalisar Dokokin Kano da wasu mutum shida sun kasance wadanda ake kara.

Zaben
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D Tofa
Asali: Facebook

A cikin karar CA/KN/233/2024, Majalisar Dokokin Kano karkashin jagorancin babban lauya Cif Adegboyega Awomolo (SAN), sun roki kotun daukaka kara ta soke hukuncin da kotun tarayya ta yanke a baya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

Kano: NNPP ta kalubalanci hurumin kotu

Awomolo ya ce kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron karar, yana mai bayyana cewa karar da Aminu Tiga da APC suka shigar ta riga ta wuce lokacin da ya kamata a shigar da ita a bisa doka.

A ranar 22 ga Oktoba, 2024, Mai shari’a Simon Amobeda na kotun tarayya ya hana KANSIEC gudanar da zaben kananan hukumomi a cikin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

A hukuncin nasa, alkalin ya ce 'yan hukumar zaben suna da katin shaidar 'yan jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar, lamarin da ya saba wa sassan 197 da 200 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kotu za ta yi hukunci kan zaben Kano

Saboda rashin jin dadin wannan hukunci, Majalisar Dokokin Jihar Kano da sauran wadanda abin ya shafa sun garzaya kotun daukaka kara.

Sun shaidawa kotu cewa harkokin zaben kananan hukumomi na a karkashin ikon jihar ne, don haka kotun jiha ce kadai ke da ikon sauraren irin wannan kara ba kotun tarayya ba.

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi

Bayan sauraron dukkan hujjoji a ranar Talata, kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a Georgewill Ekanem ya bayyana cewa kotun ta shirya yanke hukunci.

Ya bayyana cewa za a sanar da ranar da za a fitar da hukuncin ga dukkannin koken masu ruwa da tsaki a batun.

Hukuncin kotu kan kudin kananan hukumomin Kano

A baya, kun samu labarin cewa babbar kotu da ke Kano ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Musa Muhammad ta bayar da umarni na wucin gadi kan kudin kananan hukumomin Kano.

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari'a Ibrahim Musa ya hana gwamnatin tarayya yin katsalanda a kuɗin da ake bai wa ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano a kowane wata.

Ya kuma amince wa masu shigar da ƙara da su miƙa takardun kotu ga manyan hukumomin tarayya da suka haɗa da Ofishin Akanta Janar na Ƙasa da Babban Bankin Najeriya (CBN).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng