Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Zamfara, Shaguna Sama da 50 Sun Kone Kurmus

Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Zamfara, Shaguna Sama da 50 Sun Kone Kurmus

  • Rahoto ya nuna cewa gobara ta tashi a sashen masu maganin gargajiya a babbar kasuwar Zamfara, ana zancen shaguna 55 su ka kone kurmus
  • Shugaban kasuwar, Alhaji Sa’adu Dahiru ya bayyana yadda ‘yan kasuwa rasa dukiyarsu, ciki har da wanda kayan shagonsa suka kai N12m
  • Hukumomi sun ce ana binciken musabbabin gobarar, sannan an haramta amfani da wuta a harabar kasuwar domin dakile sake faruwar hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Mummunar gobara ta tashi a cikin babbar kasuwar jihar Zamfara, inda aka ce shaguna akalla 55 suka kone kurmus.

Rahotanni sun bayyana cewa, bangaren 'yan magani na cikin babbar kasuwar ne ya kama da wuta, kuma 'yan kasuwar sun kirga asara mai yawa.

'Yan kasuwa sun yi magana da gobara ta babbake shaguna 55 a babbar kasuwar Zamfara
Gobara ta babbake shaguna 55 a babbar kasuwar Zamfara, an nemi gwamnati ta kai dauki. Hoto: @Fedfireng
Asali: Getty Images

Gobara ta kone shaguna 55 a kasuwar Zamfara

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan gobarar ta afku ne a safiyar ranar Talata, kuma tana zuwa ne makonni shida bayan gobara ta kone shaguna 103 a cikin kasuwar.

Kara karanta wannan

Trump: Amurka ta yi korafi bayan Najeriya ta cire tsoro ta hana shigo da kayanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, ba a gano musabbin tashin wannan gobarar ba da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Talata.

Wani daga cikin wadanda shagunansu suka kone, kuma shugaban 'yan kasuwar, Alhaji Sa’adu Dahiru ya tabbatar da cewa kimanin shaguna 55 wutar ta lalata.

"Ba iya bangaren 'yan magani gobarar ta shafa ba, ta babbake wasu shaguna na masu sayar da riguna da kayan hadin abinci," a cewar Alhaji Sa'adu.

"Mutane sun rasa dukiyarsu" - Alhaji Sa'adu

Alhaji Sa’adu Dahiru ya bayyana wannan gobarar a matsayin babban iftila'i, yana mai cewa wasu ‘yan kasuwar sun rasa komai da suka mallaka.

"Akwai wadanda na sani da suka rasa komai a wannan gobarar. Suna da iyali da suka dogara da wannan kasuwancin, yanzu sun rasa komai.
"Akwai wani mai shago da ya ajiye N50,000 a cikin shagonsa da nufin kai su banki a yau (Talata), amma gobarar ta kone kudin tare da kayan shagonsa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata a sani game da ranar 'yan sanda ta farko a Najeriya

"Ina amfani da wannan damar in yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da ta nufi girman Allah ta kawo wa 'yan kasuwar nan dauki, ta tallafa masu da jari."

- Alhaji Sa'adu.

'Dan kasuwa ya rasa dukiyar N14m

Wani wanda abin ya shafa, Muhammad Kabiru, ya ce ya yi asarar kayayyakin da darajarsu ta kai Naira miliyan 14.

"Na dauki hakan a matsayin kaddara daga Allah. Lallai wannan jarabawa ce daga Allah, kuma dole ne mu yi imani da ita. Ina rokon gwamnatin jiha ta kawo mana dauki.
"Ba wai muna neman gwamnati ta biya mu asarar da muka yi ba ne, kuma ba wai muna neman a ba mu wasu makudan kudi ba ne, a'a, mu dai neman abin da za mu sake tayar da jari ne."

- Muhammad Kabiru.

An haramta amfani da wuta a cikin kasuwa

'Yan kasuwa sun fadi irin asarar da suka tafka da gobara ta tashi a babbar kasuwar Zamfara
An roki gwamnati ta kai dauki ga 'yan kasuwar da gobara ta babbake shagunansu a kasuwar Zamfara. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Daraktan gudanarwa na kasuwar, Alhaji Ahmad Salihu Shinkafi, ya ce ana bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

Alhaji Ahmad ya ce:

"Daga abin da muka ji daga wasu 'yan kasuwa, wasu kaucen magunguna ne suka kama da wuta saboda ba su da juriyar zafi. Sun ce idan zafi ya yi masu yawa, sai su kama da wuta. Amma dai muna kan bincike don gano gaskiyar batun."

Dangane da matakan da aka dauka don dakile faruwar hakan a gaba, daraktan gudanarwar ya ce sun haramta amfani da wuta a cikin harabar kasuwar.

"Wannan ne ma dalilin da ya sa ba mu yarda masu sayar da shayi, abinci da duk sana'ar da ta shafi amfani da wuta zuwa kusa da kasuwar ba. Allah ne kadai ya san dalilin tashin wannan gobarar."

- Alhaji Ahmad.

Gobara ta lakume shaguna a kasuwar Gusau

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an samu mummunar gobara a sashen masu sayar da kayan daki da ke cikin babbar kasuwar Gusau a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, Attajirin da ya kafa bankin Diamond, ya jagoranci MTN ya rasu

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:00 na dare, inda ta lalata shaguna da dama tare da haddasa asarar dukiya mai tarin yawa.

Kwamandan hukumar kashe gobara ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa wani mai shago ya rasa ransa a yunkurinsa na kashe gobarar da karfi da yaji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng