Gwamna Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Plateau

Gwamna Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Plateau

  • Gwamnan jihar Plateau ya yi magana da babbar murya kan hare-haren da ake kai wa a wasu ƙananan hukumomin jihar
  • Caleb Mutfwang ya bayyana cewa hare-haren da ake ksi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, ana kai su ne da manufar ƙare dangi
  • Gwamnan ya nuna cewa akwai masu daukar nauyin ƴan ta'adda domin su tayar da fitina a jihar da aka rasa rayuka rututu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Muftwang, ya yi magana kan hare-haren ta'addanci da ake kai wa a jihar.

Gwamna Caleb Mutfwang ya ce hare-haren da ake kai wa kan bayin Allah, ɗaukar nauyinsu ake yi kuma ana kai su ne da manufar kisan ƙare dangi.

Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamnan Plateau ya ce akwai masu daukar nauyin hare-hare a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Gwamnan Mutfwang ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Filato ya fayyace komai, an ji yawan garuruwan da 'yan ta'adda suka mamaye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahara dai sun kai farmaki a wasu ƙauyuka da ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Plateau, inda suka raba mutane da muhallansu tare da kashe wasu da dama.

Su wanene ke ɗaukar nauyi ta'addanci a Plateau?

Gwamna Muftwang, wanda ya nuna fushinsa bisa kashe-kashen, ya danganta hare-haren da wasu ƙungiyoyin ta’adda da bai ambaci sunayensu ba.

A cewarsa, hare-haren da ake kai wa a jihar, ɗaukar nauyinsu ake yi kuma suna da nufin shafe wasu al’ummomi daga doron ƙasa.

“Zan faɗa muku gaskiya cewa babu wani bayani da zan iya yi a kan kashe-kashen face cewa kisan ƙare dangi ne da ƴan ta’adda ke ɗaukar nauyinsa."
"Tambayar ita ce, su waye ke ɗaukar nauyin wannan ta’addanci? Wannan ne abin da dole hukumomin tsaro su taimaka wajen gano gaskiyar lamarin."
“Dole mu ɗauki matakin da za mu san masu ɗaukar nauyin wannan ɗanyen aiki, domin ba abin da wasu tsirarun mutane ke yi ba ne."

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun kai hare-haren ramuwar gayya a Zamfara, sun yi barna

"Ana ɗaukar nauyinsa ne daga wani wuri, kuma ina da tabbacin cewa a cikin kwanaki masu zuwa, hukumomin tsaro za su haɗa kai ba tare da saɓani ba, don su fito da bayanan sirri da za su taimaka mana mu magance wannan matsala."

- Gwamna Caleb Mutfwang

Caleb Mutfwang
Gwamna Mutfwang ya ce hare-haren Plateau kisan kare dangi ne Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Ƴan bindiga sun kori mutane a Plateau

Ya bayyana cewa sama da ƙauyuka 64 a jihar sun faɗa hannun ƴan bindiga da suka tilastawa mutane barin gidajensu.

“A halin da nake magana da ku yanzu, akwai aƙalla ƙauyuka 64 da ƴan ta’adda suka ƙwace a Plateau, musamman tsakanin Bokkos, Barkin Ladi da ƙaramar hukumar Riyom."
“An ƙwace su, an sake musu suna, kuma mutane na zaune a wuraren da suka kori waɗanda suka fi cancanta da su zauna a wurin.”

- Gwamna Caleb Mutfwang

Ƴan ta'adda sun tare sakataren gwamnatin Plateau

A wani labari kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda sun farmaki sakataren gwamnatin jihar Plateau, Arch. Samuel N. Jatau.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya tsage gaskiya, ya fadi fargabarsa kan 'yan Boko Haram

Ƴan ta'addan sun yi wa ayarin motocin sakataren gwamnatin jihar kwanton ɓauna ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ƙaramar hukumar Bokkos.

Samuel Jatau wanda ke cikin tawagar, ya tsallake rijiya da baya bayan jani'an tsaro sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel