'Yan Sanda, Ƴan Banga Sun Hadu Sun Yi Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar Katsina

'Yan Sanda, Ƴan Banga Sun Hadu Sun Yi Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar Katsina

  • ‘Yan sanda da hadin gwiwar 'yan banga sun ceto mutane har bakwai da aka sace a jihar Katsina, bayan sun yi artabu da ‘yan bindiga
  • Kakakin ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya ce an jami'ai sun kai dauki cikin gaggawa da aka ce an farmaki Dutsinma da Malumfashi
  • A Dutsinma, an ceto mata biyar, sai a Malumfashi, ‘yan sanda suka kubutar Hafsat Amadu da Musa Sani bayan fafatawa da ‘yan ta'addan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya, sun yi musayar wuta mai zafi da 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Katsina.

An rahoto cewa, 'yan sandan sun yi kulin-kulin Kubura da 'yan ta'addar a lokacin da suka kai farmakin sace mutane a kauyen Kurba da ke Kankara.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata a sani game da ranar 'yan sanda ta farko a Najeriya

'Yan sanda sun magantu da suka ceto mutane 7 da aka sace a Katsina
'Yan sanda da jami'an tsaro sun ceto mutane 7 da aka sace a Malumfashi da Dutsinma, jihar Katsina. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa dakarun 'yan sandan na ofishin 'yan sanda na karamar hukumar Dutsinma ne suka kai dauki lokacin da aka sace mata biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun kubutar da mata 5 a Katsina

An ce 'yan bindigar sun kai harin ne a ranar Litinin, inda suka yi nasarar yin garkuwa da mata biyar, amma kafin su yi nisa, jami'ai suka cimmasu.

Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, mai magana da yawun 'yan sandan, Abubakar Sadiq, ya shaida cewa an ceto matan da aka sace, kuma su koma ga iyalansu.

Abubakar Sadiq ya ce:

"Jami'anmu sun ceto mata biyar. 'Yan bindigar sun kai hari garin da kusan tsakar dare. Mun amsa kiran gaggawa, kan farmakin, kuma mun kai dauki cikin gaggawa, wanda hakan ya sa aka ceto wadanda aka sace, bayan an yi musayar wuta."

'Yan bindiga sun farmaki kauyukan Malumfashi

Yayin da kakakin 'yan sandan ya ce sai da aka yi musayar wuta tsakanin jami'an rundunar da 'yan bindigar, ya kuma tabbatar da cewa "mun yi nasarar ceto matan da aka sace."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

A wata arangama da ta gudana tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga a ƙaramar hukumar Malumfashi, jami'an sun ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su.

Hafsat Amadu da Musa Sani ne aka sace bayan ’yan bindiga sun kai hari kauyukan Gidan Filoti da Gidan Mairabo.

'Yan sanda sun ceto mutane biyu a Malumfashi

'Yan sanda sun magantu da suka ceto mutane 7 a garuruwa daban daban na Katsina
Katsina: Yadda jami'an tsaro suka ceto mutane 5 a Dutsinma da wasu 2 a Malumfashi. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mai sharhi kan al'amuran tsaro a Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a rahoton da ya wallafa a shafinsa na intanet.

Ya rahoto cewa:

“Bayan samun rahoto, DPO na Malumfashi ya jagoranci haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin Burdugau, wanda ake zargin mafakar ’yan bindiga ce.
“Jami’an tsaro sun fafata da ’yan bindigar, lamarin da ya sa suka tsere da raunukan harbin bindiga tare da barin mutanen da suka sace.
“An ceto Hafsat da Musa ba tare da sun samu wani rauni ba, kuma an mayar da su hannun iyalansu.”

Kara karanta wannan

Tirkashi: Ƴan ta'adda sun farmaki ofishin jam'iyyar LP, sun sace makudan kudi

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an rundunar ‘yan sandan Katsina sun samu nasarar dakile hare-haren ‘yan bindiga a wurare biyu da ke fama da matsalar tsaro.

An ce ‘yan sanda sun kuɓutar da mutane 18 da ‘yan bindiga suka sace a hanyar Funtua zuwa Gusau, bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin.

Haka kuma, jami’an tsaro sun tarwatsa wani yunkuri na satar shanu masu yawa, inda suka yi artabu da ‘yan bindiga, lamarin da ya kai ga musayar wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng