Ba a Gama Rikici ba, Sanusi II Ya ba Ɗansa Sarauta, Ya Nada Sabon Galadiman Kano

Ba a Gama Rikici ba, Sanusi II Ya ba Ɗansa Sarauta, Ya Nada Sabon Galadiman Kano

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi sababbin nade-nade a masarauta, ciki har da ɗansa Adam Lamido Sanusi (Ashraf)
  • Sanarwa daga shafin Sanusi II Dynasty ta bayyana cewa an nada Ashraf Sanusi a matsayin sabon Tafidan Kano ranar Talata 8 Afrilu, 2025
  • Nade-naden sun hada da Munir Sanusi Bayero daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano, Kabiru Tijjani Hashim daga Turakin Kano zuwa Wambai
  • Sauran sun hada da Mahmud Ado Bayero daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano, da Alhaji Ahmed Abbas Sanusi a matsayin sabon Yariman Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi sababbin nade-nade a masarautu jihar a yau Talata 8 ga watan Afrilun 2025.

Sarki Sanusi II ya yi nade-nade masu muhimmanci a masarautar ciki har da ɗansa a matsayin Tafidan Kano.

Kara karanta wannan

Shugaban 'yan sanda ya janye gayyatar Sanusi II zuwa Abuja, ya ba da sabon umarni

Sanusi II ya yi sababbin nade-nade a masarautar Kano
Sarki Sanusi II ya naɗa ɗansa, Adam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a shafin Facebook a yammacin yau Talata 8 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun janye gayyatar Sanusi II Abuja

Wannan nadin sarautar na zuwa ne bayan Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Shugaban ƴan sandan ya ce an janye gayyatar da aka yi wa Sanusi II zuwa Abuja ne bayan masu ruwa da tsaki sun shiga cikin lamarin.

Duk da haka, Kayode Egbetokun ya umarci wata tawaga ta musamman da taje Kano domin samo bayanai wajen Sanusi II kan abubuwan da suka faru wajen bikin Sallah.

Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sanusi II
Yan sanda sun fadi dalilin fasa gayyatar Sarki Sanusi II zuwa Abuja. Hoto: Nigeria Police Force, Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Sababbin nade-nade da Sarki Sanusi II ya yi

A cikin sanarwar, basaraken ya amince da nadin Alh Munir Sanusi Bayero, daga Wamban Kano zuwa Galadiman kano.

Kara karanta wannan

'Mene amfanin kwamishinan yan sandan Kano?' An soki gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

Sai kuma Alh Kabiru Tijjani Hashim wanda aka sauya daga Turakin Kano zuwa Wamban Kano.

Sannan akwai nadin Alh Mahmud Ado Bayero daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano da sauran sababbin nade-nade da sauye-sauye da basaraken ya yi.

Sanarwar ta ce:

"Masarautar Kano ta tabbatar da nadi da kuma sauye-sauye na sabbin hakimai kamar haka:
"Alh Munir Sanusi Bayero, daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano sai Alh Kabiru Tijjani Hashim, daga Turakin Kano zuwa Wamban Kano.
"An nada Alh Mahmud Ado Bayero, daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano da Adam Lamido Sanusi (Ashraf) sabon Tafidan Kano.
"Alhaji Ahmed Abbas Sanusi kuma shi ne Sabon Yariman Kano."

Sanusi II: Peter Obi ya soki gayyatar 'yan sanda

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya jinjinawa rundunar ‘yan sanda bisa janye gayyatar da ta yi wa Muhammadu Sanusi II.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Obi ya ce akwai hikima a cikin matakin da 'yan sanda suka dauka, musamman ganin irin yanayin rashin kwanciyar hankali a kasar.

Peter Obi ya kuma bukaci a bar manyan jami’an tsaro na jihohi da yankuna su rika warware irin wadannan matsaloli domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel