Gwamna Uba Sani Ya Dauko Hanyar Faranta Ran Ma'aikatan da Suka Yi Ritaya a Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ga waiwayi ƴan fansho da ma'aikatan da suka rasu da waɗanda suka yi ritaya
- Uba Sani ga ba da umarnin fitar da N3.8bn domin biyansu haƙƙoƙinsu bayan sun yi ƙorafi kan wahalhalun da suke fama da su
- Gwamnan ya bayyana cewa ya ƙudiri aniyar faranta ran tsofaffin ma'aikata waɗanda suka yi wa jihar Kaduna hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayar da umarnin fitar da kuɗaɗe domin biyan ƴan fansho haƙƙoƙinsu.
Gwamna Uba Sani ya ba da umarnin fitar da Naira biliyan 3.8 ga hukumar kula da fansho ta jihar Kaduna domin biyan kudin giratuti da haƙƙoƙin ma'aikatan da suka rasu.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Babban basaraken Igbo ya gargadi 'yan Arewa kan kisan mafarauta a Edo? An ji gaskiya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Uba Sani zai biya ƴan fansho kuɗinsu?
A cewar sanarwar, an yanke shawarar sakin kuɗin ne saboda tausayi, bayan ƙorafe-ƙorafen da aka samu daga tsofaffin ma’aikata da iyalan ma’aikatan da suka rasu.
Tsofaffin ma'aikatan dai sun bayyana cewa aikin tantancewar da ake yi yanzu ya sanya suna fuskantar matsananciyar wahala.
“Mun ƙuduri aniyar kula da jin daɗin tsofaffin ma’aikatanmu, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar Kaduna hidima."
"Dole ne mu ba su cikakken goyon bayan da zai faranta musu rai yayin da suka yi ritaya."
- Gwamna Uba Sani
A cewar gwamnan, aikin tantancewar da ake yi na da nufin kawar da “ƴan fansho na bogi” daga cikin jerin waɗanda ake biya, domin tabbatar da biyan kuɗin fansho na wata-wata ba tare da tangarɗa ba.
“Tantancewar na da nufin kawar da masu karɓar fansho ba bisa ƙa’ida ba daga cikin waɗanda ake biya domin hana asarar ƴan kuɗaɗen da jiharmu ke da su."
“Duk da haka, mun damu kan halin da masu fansho na gaskiya ke ciki, shi ya sa muka bayar da umarnin gaggauta biyan su kuɗin giratuti, haƙƙoƙin waɗanda suka rasu da sauran haƙƙokinsu da suka taru."
- Gwamna Uba Sani.

Asali: UGC
Uba Sani ya kuɗiri aniyar kula da ƴan fansho
Tun bayan hawansa kan mulki a watan Mayu 2023, Gwamna Uba Sani ya biya jimillar Naira biliyan 6.6 a matsayin kuɗin giratuti da haƙƙoƙin waɗanda suka rasu.
Hakan na nuna ƙudurin gwamnatinsa na tallafa wa tsofafɗin ma’aikata da suka ajiye aiki.
“Mun ƙuduri aniyar kula da jin daɗin ma'aikatan da suka yi ritaya, kuma za mu ci gaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa suna karɓar haƙƙokinsu ba tare da wata matsala ba."
- Gwamna Uba Sani
Gwamna Uba Sani zai ɗauki ma'aikata a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani za ta ɗauki ma'aikata.
Gwamnatin za ta ɗauki ma'aikatan lafiya guda 1,800 waɗanda za su yi aiki a cibiyoyin lafiya matakin farko da ke faɗin jihar.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar wacce ta sanar da hakan, ta kuma ƙara da cewa za a ɗaga darajar cibiyoyin lafiya matakin farko a jihar.
Asali: Legit.ng