Abubuwan da Ya Kamata a Sani game da Ranar 'Yan Sanda Ta Farko a Najeriya

Abubuwan da Ya Kamata a Sani game da Ranar 'Yan Sanda Ta Farko a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ware ranar 7 ga watan Afrilu na kowace shekara domin yin bikin ranar 'yan sanda na kasa.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta shafe kwanaki tana gudanar da bukukkuwa domin murnar ranar 'yan sanda ta kasa.

'Yan sanda sun gudanar da ayyuka da suka hada da duba marasa lafiya kyauta daga ranar 2 zuwa 7 ga watan Afrilun 2025.

Ranar yan sanda
An gudanar da bikin ranar 'yan sanda na farko a Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force|Shiisu Adam Lawal
Asali: Facebook

Yayin da aka kammala bikin ranar 'yan sanda ta kasa a ranar 7 ga Afrilu, Legit ta hada muku rahoto na musamman domin fahimtar abubuwa game da ranar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan sani game da ranar 'yan sanda

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya ayyana ranar 'yan sanda a ranar 19 ga Afrilu, 2024, yayin bikin karrama jami’an ‘yan sanda a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

An ayyana ranar ne domin ta kasance alamar tunawa da sadaukarwa da gudumawar da jami’an ‘yan sanda ke bayarwa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa za ta zama dandalin karrama jami’an da suka nuna bajinta da sadaukarwa har suka rasa rayukansu a bakin aiki.

Rundunar ta wallafa a Facebook cewa IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya tabbatar da cewa rundunar na ci gaba da jajircewa wajen kyakkyawan aiki da hidima ga kasa.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su halarci bikin domin girmama jaruman ‘yan sanda da kuma kara dankon zumunci tsakanin jami’an tsaro da al’umma.

Ranar 'yan sanda: Ayyukan da aka yi

1. Duba marasa lafiya a kyauta

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta gudanar da babban shirin agajin lafiya kyauta ga jama’ar jihar a Dutse domin bikin ranar ‘yan sanda ta kasa.

Kara karanta wannan

Matasa sun rikita Abuja da zanga zanga, an fara harba barkonon tsohuwa

An gudanar da gwaje-gwaje kamar na hawan jini, ciwon siga da na zazzabin cizon sauro, da kuma rabon magunguna da gidajen sauro.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya ce shirin wani bangare ne na kara kusanci da al’umma da inganta dangantaka tsakanin jama’a da jami’an tsaro.

Yan sanda
'Yan sanda suna duba marasa lafiya a jihar Jigawa. Hoto: Shiisu Adam Lawal
Asali: Facebook

2. Tsaftace muhalli

A ci gaba da bukukuwan bikin Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa, Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Jigawa ta gudanar da wani shirin tsaftace muhalli a ranar Juma’a, 4 ga Afrilu, 2025.

An gudanar da aikin ne a manyan wurare da suka hada da titin Hakimi, ‘Yan Tifa da tsohuwar kasuwa, inda jami’an ‘yan sanda suka shiga sahun gaba wajen share tituna da kwashe shara.

Aikin na daga cikin jerin abubuwan da rundunar ta shirya a bikin Ranar ‘Yan Sanda, domin nuna jajircewar jami’an tsaro wajen ba da gudumawa ga ci gaban al’umma.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya ce tsaftar muhalli na daya daga cikin hanyoyin kare lafiyar al’umma da kuma kara dankon zumunci tsakanin jami’an tsaro da jama’a.

Kara karanta wannan

An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

'Yan sanda
'Yan sanda na shara a jihar Jigawa. Hoto: Shiisu Adam Lawal
Asali: Facebook

3. Tafiya domin motsa jiki

A ci gaba da shirin bikin Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa, rundunar ‘yan sanda ta gudanar da wata gagarumar tafiya kai a jihohi 36 da Abuja a safiyar Asabar, 5 ga Afrilu, 2025.

Tafiyar, wadda ta fara tun daga karfe 6:00 na safe, ta samu halartar jami’an ‘yan sanda daga dukkan matakai tare da fararen hula masu goyon bayan aikin ‘yan sanda.

Rundunar 'yan sanda ta wallafa a Facebook cewa hakan na daga cikin shirye-shiryen karshe da ta yi a bikin ranar 'yan sanda da aka gudanar a Eagle Square, Abuja, a ranar 7 ga Afrilu.

Tafiyar ta kasance wata hanya ta karfafa zumunci da fahimtar juna tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin da suke yi wa hidima.

Yan sanda
Yan sanda sun gudanar da tafiya a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wa 'yan sanda alkawari

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta gina ‘yan sanda kwararru masu amfani da fasahar zamani domin yaki da laifuffuka a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, yayin bikin kammala makon Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa da aka gudanar a Eagle Square, Abuja.

A jawabin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya karanta a madadinsa, Tinubu ya ce:

“Wannan gwamnati za ta ci gaba da daukar walwala da jin dadin jami’an ‘yan sanda da muhimmanci.
"Za mu tabbatar da cewa rundunar tana da kayan aiki na zamani, horo mai nagarta da kuma albashi mai kyau da ya dace da aikin da kuke yi.”
Shettima
Mataimakin shugaban kasa tare da sufeton 'yan sanda na kasa. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

A sakon da ma'aikatar yada labarai ta wallafa a X, Tinubu ya ce zai tabbatar da samar da matsuguni, kula da lafiya da kuma ingantaccen ilimi ga ‘ya’yan jami’an ‘yan sanda.

'Yan sanda sun kwantar da tarzoma a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta kwantar da tarzoma a jihar Bauchi a ranar Juma'a da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kamar a Jahiliyya: An tono gawa bayan mahaifi ya kashe, ya birne 'yarsa a Najeriya

An fara samun tashin hankali ne a wani masallaci a unguwar Jahun yayin da wani limami ya yi mummunar magana a kan marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi.

Bayan shawo kan lamarin, kwamishinan 'yan sandan jihar ya gargadi malamai kan amfani da lafuzan da za su iya jawo tashin hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel