Wata Sabuwa: Ƴan Ta'adda Sun Farmaki Ofishin Jam'iyyar LP, Sun Sace Makudan Kudi
- Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari sakatariyar jam’iyyar LP da ke Legas, suka sace kuɗi da kayayyaki masu mahimmanci
- Wani ma’aikaci ya ce kimanin mutum 300 suka farma ofishin da safiyar Litinin, suka tafka satar kuma suka tsere kafin zuwan ‘yan sanda
- Wannan na zuwa ne da jam’iyyar LP ta zargi Gwamna Alex Otti da cin amanar jam’iyya, ta kuma yi gargaɗi ga Peter Obi kan rashin biyayya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Wasu da ake zargin ‘yan ta'adda ne sun farmaki sakatariyar LP da ke Ikeja GRA, jihar Legas, a ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025.
An rahoto cewa 'yan ta'addar da suka mamaye ofishin jam'iyyar, sun kwashe muhimman kayayyaki da makudan kudade, sannan suka arce kafin zuwa jami'an tsaro.

Asali: Twitter
'Yan ta'adda sun farmaki sakatariyar LP
Wani ma’aikaci a sakatariyar ya bayyana cewa kimanin mutum 300 ne suka farmaki wurin da misalin karfe 10:00 na safiya ranar, inji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikacin ya shaida cewa 'yan ta'addar sun lalata ofisoshin sakatariyar, sannan suka kwashe takardu, makudan kudi, da wasu kayayyaki masu daraja.
‘Yan sanda sun isa wurin da abin ya faru jim kadan bayan harin, amma sun kasa cafke ko da mutum daya daga cikin wadanda suka kai harin, kasancewar sun tsere kafin isowarsu.
Vanguard ta rahoto cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san musabbabin kai harin ba.
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an fara bincike domin gano wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
LP ta zargi gwamna da cin amanar jam'iyya
Wannan harin na zuwa ne yayin da kwamitin NEC na jam’iyyar LP ya zargi gwamnan jihar Abia, Alex Otti, da aikata wasu ayyuka na cin amanar jam’iyya.
Sakataren jam’iyyar na kasa, Ibrahim Umar-Farouk, ne ya karanta sanarwar da aka fitar a karshen taron da NEC ta gudanar, wadda aka wallafa a shafin LP na X.
A cewar sanarwar, NEC ta zargi Gwamna Alex Otti da kira taron da bai samu amincewar jam’iyya ba tare da kokarin kwace ikon majalizar zartarwar.
Jam’iyyar ta kuma zargi Otti da goyon bayan wata jam’iyyar daban a zabukan kananan hukumomi da suka gudana a jihar Abia.
“Wadannan ayyuka na cin amanar jam’iyya da gwamna ke yi sun sabawa halayen shugaba nagari, kuma ba za a yarda da su ba,” in ji sanarwar.
LP ta gargaɗi Peter Obi da wasu jiga-jigan jam’iyya

Asali: Twitter
Kwamitin NEC ya ce za a dauki matakin ladabtarwa kan Gwamna Otti bisa wadannan zarge-zarge, daidai da sashe na 19 na kundin tsarin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma yi gargadin cewa za ta dauki mataki kan duk wani mamba da ya karya dokar jam’iyyar, komai girman mukaminsa ko tasirinsa.
Haka kuma, NEC ta yi gargadi ga ɗan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, da kada ya aikata wani abu da zai iya kawo rarrabuwar kai ko rikita jam’iyyar.
“NEC ta yi gargaɗi ga tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da kada ya shiga wani abu da zai dagula zaman lafiya da hadin kan jam’iyyar. Idan aka same shi da laifi, za a dauki matakin ladabtarwa mai tsauri a kasan."
- Ibrahim Umar-Farouk.
Dan takarar LP ya sauya sheka zuwa PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ɗan takarar gwamna na Enugu a zaɓen 2023, Chief Chijioke Edeoga, ya koma jam’iyyar PDP bayan barin LP da ya tsaya tikitin ta.
Edeoga ya ce dawowarsa PDP na da alaƙa da jajircewar Gwamna Peter Mbah da kuma irin kyakkyawan shugabanci da yake baiwa jihar Enugu.
Shugaban PDP na jihar, Dr. Martin Chukwunweike, ya bayyana wannan sauyi a matsayin nasara ga jam’iyyar, yana mai roƙon sauran 'yan jam’iyya su dawo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng